Hisbah ta sulhunta ma'aurata 3,579 da wasu a Jihar Jigawa

Hisbah ta sulhunta ma'aurata 3,579 da wasu a Jihar Jigawa

  • Hukumar Jami'an tsaro na musulunci wato Hisbah ta Jihar Jigawa ta ce ta yi sulhu tsakanin ma'aurata da wasu mutane 3,579 a shekarar 2021
  • Kwamandan hukumar na Jigawa, Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hakan yayin hirar da NAN ta yi da shi a Dutse, ranar Alhamis
  • Ibrahim Dahiru ya ce sulhunta al'umma na cikin manyan ayyukan da hukumar ke yi, yana mai cewa musulunci na goyon bayan sulhu

Jihar Jigawa - Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta ce ta sulhunta ma'aurata 3,579 a shekarar 2021, a cewar kwamandan hukumar, Malam Ibrahim Dahiru, The Nation ta ruwaito.

Dahiru ya bayyana hakan ne cikin hirar da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta yi da shi a Dutse, a ranar Alhamis.

Hisbah ta sulhunta ma'aurata 3,579 da wasu a Jihar Jigawa
Jigawa: Hisbah ta sulhunta ma'aurata 3,579 da wasu mutanen. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Jihar Neja: Shugaban karamar hukuma ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe mutane a masallaci

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dahiru ya yi bayanin cewa yin sulhu tsakanin ma'aurata domin tabbatar sun zauna lafiya yana daga cikin manyan nauyin da ya rataya a kan hukumar.

Ya ce hukumar ta kuma taimaka wurin yin sulhu tsakanin yan kasuwa 41, iyaye da yaransu 221, makwabta 319 da makiyaya da manoma 71, rahoton The Nation.

Kwamandan ya ce:

"Yin sulhu yana taimakawa wurin warware matsaloli da gina zaman lafiya tsakanin al'umma.
"Hukumar tana da kwararun ma'aikata da ke da basira da fahimtar yadda ake in sulhu tsakanin mutane.
"Ina son in yi amfani da wannan damar in jadada cewa musulunci na goyon bayan sulhu, don haka sulhu ya fi alheri a maimakon zuwa kotu.
"Kazalika, sulhu na da kyau saboda babu bata lokaci da kayan aiki. Kuma ba a tilastawa kowa ya amince da sulhu, tana yiwuwa ne kawai idan bangarorin biyu sun amince."

Kara karanta wannan

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

Ya ce babban aikin hukumar itace tabbatar da cewa mutane sun zauna lafiya da juna ba tare da la'akari da addini, shekaru, sana'a ko jinsinsu ba.

'Yan Hisbah sun kwace kwalaben giya 389 a Jigawa

A wani labarin daban, Jami'an Hisbah na jihar Jigawa ta ce ta kama wata mota kirar Sharon dauke da kwalaben giya 389 a jihar.

Kwamandan Hisbah na jihar, Ibrahim Dahiru, ne ya bayyana hakan yayin wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Dutse a ranar Laraba.

Dahiru ya ce an kama motar ne yayin wata sumame misalin karfe 10 a ranar 1 ga watan Oktoba a karamar hukumar Hadejia na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel