'Yan Hisbah sun kwace kwalaben giya 389 a Jigawa

'Yan Hisbah sun kwace kwalaben giya 389 a Jigawa

Jami'an Hisbah na jihar Jigawa ta ce ta kama wata mota kirar Sharon dauke da kwalaben giya 389 a jihar.

Kwamandan Hisbah na jihar, Ibrahim Dahiru, ne ya bayyana hakan yayin wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Dutse a ranar Laraba.

Dahiru ya ce an kama motar ne yayin wata sumame misalin karfe 10 a ranar 1 ga watan Oktoba a karamar hukumar Hadejia na jihar.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe hatsabibin mai garkuwa da mutane 'Iblis'

Ya ce an kama motar ne a kofan gidan wan Emma Rotimi da ke Mairanda Jama'a Quaters, a Hadejia.

Kwamandan ya ce 'yan Hisban sun mika mai giyar da kwalaben giyan hannun 'yan sanda domin su zurfafa bincike tare da gabatar da shi a gaban kuliya.

"Daga baya an kai su kotu," inji shi.

Dahiru ya ce an hana shan giya a dukkan sassan jihar kana ya ce hukumar ta Hisbah za ta cigaba da yaki da ayyukan asha a jihar.

Ya kuma shawarci mazauna jihar su kaucewa aikata duk wani abu da ka iya janyo tabarbarewar tarbiyar al'umma kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel