Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na wani tsohon shugabanta

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na wani tsohon shugabanta

  • Allah ya yiwa tsohon Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo, Hafeez Tijani Adiaro, rasuwa
  • Marigayin ya amsa kiran mahaliccinsa ne a yammacin ranar Litinin, 10 ga watan Janairu
  • Adiaro ya yi shugabancin karamar hukumar Irepo da ke jihar har sau uku

Oyo - Tsohon Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo, Hafeez Tijani Adiaro, ya rasu.

Sahara Reporters ya rahoto cewa Adiaro ya rasu ne a yammacin ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na wani tsohon shugabanta
Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na wani tsohon shugabanta Hoto: Punch
Asali: UGC

Zuwa yanzu ba a san ainahin abun da ya haddasa mutuwar tasa ba.

An tattaro cewa marigayin ya bayar da cikakken lokacinsa ga siyasa a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Oyo, Rasheed Ladoja.

Kara karanta wannan

Tarihin Marigayi Shonekan wanda ya yi kwana 83 a mulki, Abacha ya yi masa juyin-mulki

Adiaro ya kuma yi shugabancin karamar hukumar Irepo har sau uku.

Mahaifarsa ta Kishi shine hedkwatar karamar hukumar Irepo.

Wata majiya ta tabbatarwa da jaridar labarin mutuwar Adiaro inda ta ce:

“Ya mutu a jiya (Litinin).

Najeriya ta yi rashi: Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

A wani labarin, mun ji cewa Cif Ernest Shonekan wanda ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya wacce ta gaji mulkin Janar Ibrahim Babangida, ya rasu.

Shonekan ya rasu a jihar Legas yana da shekaru 85 a duniya, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

Ya kasance shugaban kasa Najeriya na wucin gadi tsakanin 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamba, 1993 lokacin da aka hambarar da shi a juyin mulkin da marigayi Janar Sani Abacha ya jagoranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng