2023: Babban jami'in INEC ya ajiye aikinsa, ya shiga APC don yin takarar gwamna a jihar Arewa

2023: Babban jami'in INEC ya ajiye aikinsa, ya shiga APC don yin takarar gwamna a jihar Arewa

  • An nada Nentawe Yilwatda, tsohon malami a jami’ar tarayya ta noma da kiwo da ke Makurdi a matsayin kwamishinan zabe na INEC a watan Yulin 2017 sannan aka tura shi jihar Binuwai
  • Yayin da ya yi shekaru 4 a mukamin, da shi aka gudanar da zaben jihar Binuwai, Anambra, Osun, Ribas da Cross River wadanda duk ya jagoranta
  • Sai dai a watan Disamban 2021, ya yi murabus daga mukamin nasa sannan ya koma jihar Filato don tsayawa takarar gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APC

Jihar Plateau - Bayan kwashe shekaru hudu a matsayin kwamishinan zabe (REC), Nentawe Yilwatda ya yi murabus daga mukaminsa na INEC inda ya koma siyasa, Premium Times ta ruwaito.

An nada Mr Yilwatda, tsohon lakcara a jami’ar tarayya ta noma da kiwo, Makurdi, a matsayin REC a watan Yulin 2017 sannan aka tura shi jihar Binuwai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shahararren tsohon shugaban PDP ya rasu a wata jihar arewa

Yayin shekaru hudunsa a kan mukamin, ya jagoranci zaben jihar Binuwai, Anambra, Osun, Ribas da jihar Cross River.

2023: Babban jami'in INEC ya ajiye aikinsa, ya shiga APC don yi takarar gwamna a jihar Arewa
2023: Babban jami'in INEC ya yi murabus daga aiki, ya shiga APC don yi takarar gwamna a jihar Arewa. Photo credit: Nentawe Yilwatda Goshwe
Asali: Facebook

Amma a watan Disamban 2021, tsohon lakcaran mai shekaru 53 ya yi murabus daga mukamin nasa ya koma asalin jiharsa, Filato, yankin arewa ta tsakiya, inda ya koma APC yana neman takarar gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya tabbatar wa da manema labarai cewa siyasa zai koma

A ranar Laraba, an bukaci jin ta bakin tsohon REC din inda ya ce ya yi murabus daga INEC ne saboda wasu dalilansa. Ya kuma tabbatar da cewa ya koma siyasar jam’iyya ne.

A cewarsa, har yanzu bai koma APC ba amma zai yi hakan nan kusa. INEC ta tabbatar wa Premium Times cewa tsohon lakcaran ya dade da yin murabus.

Festus Okoye, kwamishinan labaran INEC, ya ce:

Kara karanta wannan

Zulum: Mayakan ISWAP sun fi na Boko Haram makamai, dole ne a dakile su

“Eh gaskiya ne, ya yi murabus don ya bar hukumar da kansa.”

A cewar Okoye, bai san dalilin da yasa Mr Yilwatda ya bar hukumar ba kafin lokacin da aka dibar masa ya kare.

Tuni ya fara kamfen din tsayawa gwamna

Amma Premium Times ta tabbatar da cewa ya yi murabus ne don ya tsaya takarar gwamnan jihar Filato.

Tuni ya bazama don fara kamfen din lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC don tsayawa takarar gwamna a zaben 2023 mai zuwa.

A ranar 9 ga watan Janairu, tsohon REC din ya wallafa batun fara kamfen dinsa ta shafinsa na Facebook inda ya yi jirwaye mai kamar wanka akan samar da shugaba nagari ga jihar Filato.

Cikin datsin nan Yilwatda ya bayyana kamfen din shi inda ya kira kansa da dan takarar gwamna a 2023.

Ba shi ba ne mutum na farko da ya yi hakan ba

Kara karanta wannan

Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo

Murabus din REC din Binuwai din don rungumar siyasa ya auku ne bayan watanni 29 da wani jami’in INEC din ya yi makamancin hakan.

Frankland Briyai, wanda REC ne na jihar Cross River a watan Augustan 2019 ya yi murabus daga mukaminsa inda ya tsaya takarar gwamnan jihar Bayelsa lokacin ana saura watanni uku a yi zaben.

Ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara a harabar INEC ta Jihar Calabar, babban birnin Jihar Cross River wanda nan da nan hukumar zaben ta fusata a kan abinda ya yi.

Hukumar ta saki wata takarda wacce ta tumbuke Mr Briyai daga mukaminsa saboda amfani da harabar INEC wurin yin sanarwa a kan siyasa.

Sai dai da aka yi zaben a ranar 16 ga watan Nuwamban 2019, tsohon REC din INEC din bai bayyana cikin ‘yan takara ba don APC ba ta tsayar da shi ba.

Abinda Yilwatda ya yi bai dace ba

Abdul Mahmud, wani lauya mazaunin Abuja kuma mai rajin kare hakkin bil’adama ya ce bai dace kwamishinan INEC ya yi murabus don tsayawa takara take yanke ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna, kuma jigon jama'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

Kamar yadda ya ce:

“Irin wannan ma’aikacin ya san sirrin INEC kuma ta yuwu ya iya amfani da iliminsa wurin cin zaben.”

Lauyan ya bukaci majalisar tarayya da ta kula da irin wannan kuma ta yi gaggawar dakatar da duk wani mai babban mukami a INEC daga tsayawa takara na wani lokaci bayan sauka daga mukaminsa.

Dokar INEC ta 1998 ta hana duk wani kwamishinan hukumar daga tsayawa wata takara har sai ya yi shekaru 5 bayan sauka daga mukaminsa.

Sai dai daga baya an cire wannan dokar daga cikin dokokin zaben Najeriya.

A cewar Mahmud:

“Ya kamata a dawo da dokar ganin yadda lamurra irin haka su ke ta wakana.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel