Borno: 'Yan sanda da mafarauta sun cafke masu satar mutane 3, sun ceto mutum 1

Borno: 'Yan sanda da mafarauta sun cafke masu satar mutane 3, sun ceto mutum 1

  • Rundunar hadin guiwar 'yan sanda da mafarauta sun yi ram da wasu mutum uku da ake zargi da garkuwa da mutane a kauyen Sakasimta da ke Hawul
  • 'Yan sandan da mafarautan sun kai hari maboyar miyagun inda suka ceto wani mutum daya mai suna Manu Adamu wanda suka yi garkuwa da shi
  • Buje Jalo, Abubakar Abdullahi da Buba Manu sune wadanda aka cafke kuma suna taimaka wa 'yan sandan da bayanai domin kamo sauran abokan ta'addancinsu

Hawul, Borno - Rundunar hadin guiwa ta 'yan sanda da mafarauta sun cafke wasu mutum uku da suka kware wurin garkuwa da mutane a maboyarsu da ke kauyen Sakasimta na karamar hukumar Hawul na jihar Borno.

Daily Trust ta tattaro cewa, an yi nasarar aikin wanda ya sa aka ceto wani mutum daya mai suna Manu Adamu wanda suka yi garkuwa da shi.

Kara karanta wannan

An gurfanar da wani mutum a gaban kotu bisa kan sace yar’uwarsa a Kaduna

Borno: 'Yan sanda da mafarauta sun cafke masu satar mutane 3, sun ceto mutum 1
Borno: 'Yan sanda da mafarauta sun cafke masu satar mutane 3, sun ceto mutum 1. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno, ASP Sani Muhammed, ya tabbatar da kamen masu garkuwa da mutanen da kuma ceto mutum daya, Daily Trust ta ruwaito.

Muhammad ya bayar da sunan masu garkuwa da mutanen da aka damke da Buje Jalo, Buba Manu da Abdullahi Abubakar inda ya kara da cewa wadanda ake zargin suna taimaka wa masu bincike wurin cafko sauran wadanda suka tsere.

Ya kara da cewa, biyu daga cikin 'yan kungiyar masu garkuwa da mutanen ya tsere da daya daga cikin wanda suka sata, wanda har yanzu ba a gano sunansa ba.

Taraba: Ƴan bindiga sun sace ƴaƴan tsohon SSG 6, dogarinsu da direba

A wani labari na daban, 'yan ta'adda sun yi garkuwa da 'ya'yan tsohon sakataren gwamnatin jihar Taraba har su shida, Gebon Kataps, tare da dan sandan da ke basu kariya da kuma direbansu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

Guardian ta ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin amma bata tabbatar da yawan wadanda aka sace ba.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan, Usman Abdullahi, ya ce lamarin ya faru wurin kauyen Jamtari da ke karamar hukumar Gashaka ta jihar.

Yayin aukuwar lamarin, 'yan ta'addan sun sheke mutum daya, wani jami'in dan sanda da ke aiki a Jamtari ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel