An kuma: 'Yan bindiga sun sake sace 'yan kasuwa da dama a hanyar Birnin Gwari a Kaduna

An kuma: 'Yan bindiga sun sake sace 'yan kasuwa da dama a hanyar Birnin Gwari a Kaduna

  • Yan bindiga sun sake tare motoccin 'yan kasuwa a hanyar Birnin Gwari a Jihar Kaduna inda suka sace da dama cikinsu suka shige da su daji
  • Wani shaidan gani da ido ya ce 'yan kasuwan sun biyo hanyar ne bayan yin jerin gwano amma 'yan bindigan suka tare kimanin motocci hudu da suka fara tahowa
  • Ko a kwanakin baya yan bindigan sun tare motoccin matafiya a kauyen Udawa bayan Buruku a karamar hukumar Chikun a jihar ta Kaduna suka sace wasu

Jihar Kaduna - Wasu da ake zargin yan bindiga ne, a ranar Laraba sun sace yan kasuwa da dama da ke hanyarsu ta zuwa Kano daga karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Wani direba wanda abin ya faru a idonsa ya shaidawa Premium Times cewa 'yan bindigan sun tare babban titin ne tsakanin Birnin Gwari da dajin Unguwar Yako sannan suka sace yan kasuwan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Akalla mutum 17 sun mutu, yayin da yan bindiga suka cinnawa gidaje wuta a Filato

An kuma: 'Yan bindiga sun sake sace 'yan kasuwa da dama a hanyar Birnin Gwari a Kaduna
'Yan bindiga sun sake tare matfiya a hanyar Birnin Gwari a Kaduna, sun yi awon gaba da wasu da dama. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ganau sun tabbatar da afkuwar lamarin

Majiyoyi sun bayyana cewa dimbin mutanen da aka sace sun taso ne daga Birnin Gwari da jihohin Niger suna hanyarsu na zuwa Kano domin kasuwanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ya ce:

"Muna tafiya ne cikin tawaga tare da jami'an tsaro amma su (yan bindigan) suka tare wadanda suke gaba da jerin gwanon motoccin, hakan yasa suka yi saukin sace su.
"Mun taho mun tarar da motocci hudu ba mutane, yayin da muke tafiya mun hangi yan bindigan sun shiga daji tare da wadanda suka kama. Sojoji sun bi sahunsu, mun tsaya a wani wuri mai hatsari a daji (Unguwar Yako) yayin da jami'an tsaro da suke mana rakiya suke kokarin ceto wadanda aka sace."

An dade ana kai wa matafiya hare-hare a hanyar

Wanann harin na baya-bayan yana zuwa ne kasa da wata guda bayan sace matafiya fiye da 70 da yan bindigan suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mummunar barna

Lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan Disamban 2021 kusa da kauyen Udawa bayan Buruku a karamar hukumar Chikun a jihar ta Kaduna.

Mai magana da yawun yan sanda a Kaduna, Mohammed Jalige, bai amsa wayarsa ba da aka yi kokarin ji ta bakinsa game da afkuwar lamarin na ranar Laraba.

A halin yanzu mafi yawancin mazauna Birnin Gwari ba su iya tafiya sai da jami'an tsaro amma duk da hakan ba su tsira daga harin yan bindigan ba.

'Yan bindiga sun dira a Kano, sun sace mahaifiyar ɗan majalisa

A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Laraba sun sace mahaifiyar Isyaku Ali-Danja, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gezawa a majalisar jihar Kano.

Daily Nigerian ta rahoto cewa yan bindigan sun afka gidan mahaifiyar dan majalisar ne da ke Gezawa misalin karfe 1 na dare, suka balle kofa sannan suka yi awon gaba da ita.

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Mr Ali-Danja, wanda ya taba rike mukamin kakakin majalisa, ya ce da farko yan bindigan sun umurci mahaifiyarsa ta bude kofa amma ta ki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel