Kano: Yadda rikicin sarauta ya mamaye kauyen Langel da ke Tofa

Kano: Yadda rikicin sarauta ya mamaye kauyen Langel da ke Tofa

  • Rikici ya kacame sakamakon neman kujerar dagacin kauyen Langel da ke karamar hukumar Tofa da mazauna garin ke yi
  • Alhaji Mahmuda Langel, tsohon dagacin garin ya yi murabus saboda yawan shekaru kuma ya kwashe shekaru hamsin kan karagar mulkin
  • Sai dai ya bukaci babban dan sa ya maye gurbinsa, lamarin da ya kawo rikici inda 'yan takara suka dinga bullowa har aka yi zabe
  • Wani Alhaji Umaru ya lashe zaben, amma mazauna yankin sun ce ba a yi zaben kwarai ba, an kawo wasu sun zaba musu dagaci ne

Langel, Kano - Rikici ya kacame a kauyen Langel da ke karamar hukumar Tofa ta jihar Kano kan wanda zai zama dagacin garin.

An tattaro cewa, rikicin da ya fara kwanaki kadan da suka gabata ya yi sanadin arangama tsakanin mazauna yankin wanda hakan ya bar wasu da miyagun raunika, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

Kano: Yadda rikicin sarauta ya mamaye kauyen Langel da ke Tofa
Kano: Yadda rikicin sarauta ya mamaye kauyen Langel da ke Tofa. Hot daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon dagacin ya bukaci babban dan sa, Alhaji Abubakar Langel, da ya karba ragamar sarautar amma wasu mazauna yanki sun yi na'am da wannan hukuncin.

Kamar yadda magoya bayan Alhaji Abubakar suka sanar, ya na aiki tukuru tun kafin mahaifinsa ya yi murabus kuma mazauna yankin sun yanke hukuncin goyon bayansa wurin gadon mahaifinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito cewa, wata majiya a yankin wacce ta bukaci a boye sunanta, ta ce wadanda suke sukar hukuncin basaraken sun kawo 'yan takara biyu da za su nemi kujerar yayin zaben.

A zaben da aka yi ranar Lahadi da ta gabata, wani Alhaji Umaru ne ya lashe kuma don haka shi ne ya zama sabon dagacin.

Amma masu goyon bayan Alhaji Abubakar sun zargi cewa ba a yi zaben Allah da Annabi ba kuma sun yi kira ga masarautar Bichi da ta sake zaben.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

"Kamar yadda tsarin nadin sarautar ya ke a Langel, akwai mutum 23 da ya dace su yi zaben. Akwai Sarkin Noma, Sarkin Aska, Sarkin Fawa, Sarkin Fulani, Sarkin Kasuwa, Sankira da shugabannin gunduma 13, limamai biyu da dattawa biyu.
"Amma kuma, mutane da yawa an dauko su ne ba daga yankinmu ba kuma sune suka yi zaben," Hussaini Sankira, daya daga cikin 'yan takarar yace.
“Yayin da muka gane cewa an kawo wasu ba daga yankinmu ba, mun yi wa hakimi Alhaji Isyaku Umar Tofa korafi kuma ya sanar da cewa ba ya nan lokacin da aka yi zaben.
"Daga nan sai ya fara jin ta bakin mutane kan wanda suke so, a tattaunawar da yayi, ya ce Alhaji Umaru ne wanda ya fi dacewa da wannan matsayin kuma shi ne sabon dagacin."

Kano: Matukan adaidaita sahu sun tafka asarar N300m bayan fadawa yajin aiki

A wani labari na daban, yayin da 'yan adaidaita suka fada yajin aiki wadanda aka fi sani da 'yan sahu ko masu Napep a Kano ranar Litinin, hakan ya janyo asarar tarin dukiya ga jihar, matukan haka zalika miliyoyin kudi ga 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu a cikin shekara 1 da matukan adaidaitan suka tsaida amfani da ita wanda ya janyo ci baya ga tattalin arzirki da walwalar mazauna jihar.

An kiyasta cewa, yajin aikin da suka shiga a ranar Litinin ya janyo a kalla asarar naira miliyan 6 wanda jihar ke samun harajin kowacce rana naira 100 ga kowanne mutukin adaidaita a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel