Kano: Matukan adaidaita sahu sun tafka asarar N300m bayan fadawa yajin aiki

Kano: Matukan adaidaita sahu sun tafka asarar N300m bayan fadawa yajin aiki

Yayin da 'yan adaidaita suka fada yajin aiki wadanda aka fi sani da 'yan sahu ko masu Napep a Kano ranar Litinin, hakan ya janyo asarar tarin dukiya ga jihar, matukan haka zalika miliyoyin kudi ga 'yan kasuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu a cikin shekara 1 da matukan adaidaitan suka tsaida amfani da ita wanda ya janyo ci baya ga tattalin arzirki da walwalar mazauna jihar.

Kano: Matukan adaidaita sahu sun tafka asarar N300m bayan fadawa yajin aiki
Kano: Matukan adaidaita sahu sun tafka asarar N300m bayan fadawa yajin aiki. Hot daga dailytrust.com
Asali: UGC

An kiyasta cewa, yajin aikin da suka shiga a ranar Litinin ya janyo a kalla asarar naira miliyan 6 wanda jihar ke samun harajin kowacce rana naira 100 ga kowanne mutukin adaidaita a jihar.

A bangaren matukan adaidaitan kuwa, sun tafka asarar akalla kimanin N300,000,000, Daily Trust ta ambata wanda tace suna samun tsakanin N5,000 da N7000 a kowacce rana.

Kara karanta wannan

KAROTO ga 'yan daidaita sahun da suka shiga yajin aiki: Za ku gane shayi ruwa ne

An tattaro yadda matukan suke zanga-zanga akan karin kudin rijista da hukamar kula da tituna (KAROTA) tayi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar ta koma amsar N18,000 ga sabbin masu rijista, yayin da suka koma amsar N8,000 ga masu sabunta rijista a duk shekara.

Shugaban hukumar matuka adaidaita, Sani Sa'idu Dankoli, yace asalin matsalar da ta saka su cikin wannan yanayin shi ne yadda gwamnatin tun farko tasa N20,000 ga kowanne matukin duk shekara.

"Lokacin da muka sa baki kuma muka ki amincewa, sai suka rage kudin zuwa N8,000. Duk da haka muka nema a kara rage mana wanda har ya kusa janyo mana rabuwar dutse hannun riga da shugaban KAROTA saboda yace abin ya yi yawa.
"Gwamnatin ita da kanta ta jinjina kokarinmu na biyan harajinmu a kowacce rana. Ko dan haka, mun cancanci a sauraremu," yace.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: 'Yan a daidaita sahu sun tsunduma yajin aiki a jihar Kano

Yace har yanzu suna magana da mambobinsu dan janye yajin aikin saboda da yawansu basu da abinda za su ci da iyalansu indai basu fita sun nema kullum ba.

Sai dai mai magana da yawun KAROTA, Nabulisi Kofar Na'isa, ya bayyana adaidaita 60,000 suke biyan haraji a kowacce rana.

Yace masu adaidaita 10,000 ne suka riga suka sabunta rijistarsu, wanda yake nuna jihar ta na sa ran samun a kalla Naira miliyan 400 daga adaidaita 50,000 (N8,000 daga kowacce adaidaita), yayin da sabbin matukan ake saran su biya N18,000 kowannensu.

Yayin da Daily Trust ta zanta da wani matukin adaidaita, Muhammad Lawal Ishaq, yace ya sabunta lasisinsa amma yayi asarar tsakanin N6,000 zuwa N7,000 a kowacce rana sanadiyyar yajin aikin da aka fada.

Adamu Hamza, wani dan kasuwa a kantin Kwari a ke Kano, yace saboda rashin adaidaita sahu mutane da dama basu iya zuwa kasuwa su bude shagunansu, hakan ya nuna 'yan kasuwa sun yi asarar miliyoyin kudi saboda yajin aikin.

Kara karanta wannan

Umarnin IPOB: Za mu kaurace wa kayayyakin kudu, CNG ta ja kunne

"Sannan, ba mu ganin masu tallar abinci. Babu abinci yau a kasuwar," ya koka.

Yajin aikin da matuka adaidaitan suka fada yazo daidai da lokacin komawa makarantun firamare da sakandare a Kano, wanda yasa dalibai da dama basu je makaranta ba, wasu kuma su kai ta garari a titi basu samu abun hawa ba.

Mazauna garin wadanda suke kokarin tafiya wurin neman kudi da wurin aiki sun yi cirko-cirko saboda rashin ababen hawa.

Da safiyar ranar Litinin, kananan ababen hawa da mashinan gida ne kan titina a jihar, wadanda suka maye gurbin adaidaita gurin kai komo.

Masu adaidaita-sahu a Kano sun tsinduma yajin aiki saboda harajin N100

A wani labari na daban, fasinjoji a birnin Kano sun shiga mawuyacin hali saboda yajin aikin da masu adaidaita-sahu suka fara a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Sun fara yajin aikin ne domin nuna rashin amincewarsu da harajin N100 a kullum da gwamnatin jihar ta kakaba musu ta hannun Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa, KAROTA, da wasu batutuwan.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Masu adaidaita-sahun sun ce wannan matakin da suka dauka ya zama dole saboda abinda suka kwatanta da kwace da sunan haraji da wasu tarar da aka karba a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel