Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji

Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji

  • Sakamakon tsananin luguden wutan da jiragen NAF ke yi a Zamfara, Bello Turji da yaransa sun bar dajin Fakai da ke Shinkafi inda suka koma dajin Gando
  • Mazauna yankin sun bayyana tashin hankalin da suka fada sakamakon ganin 'yan ta'addan sun kafa tantinansu a yankin na Bukkuyum
  • Akwai tabbacin cewa, Shehu Bayade, shugaban 'yan bindigan dajin Gando ne ya aike musu da gayyata ta yadda za su samu mafaka saboda duhun dajin

Zamfara - Bello Turji, gagararren dan bindigan da ya addabi yankin arewa maso yamma, ya sauya sheka daga jihar Zamfara sakamakon tsananin luguden wutar da sojojin Najeriya ke yi musu.

Daily Trust ta ruwaito yadda sojojin saman Najeriya suka ragargaza sansanonin 'yan bindiga a samamen da suke ta kaiwa yankin.

Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji
Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, gagararen dan bindigan da mutanensa sun hanzarta barin dajin da suke saboda jiragen NAF suna ta ragargazar dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi kuma suna tafiya kudancin Zamfara.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60

Majiyoyin sun ce an hango matasan dauke da makamansu inda suka kafa tantina a dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar.

Gando yanki ne da ke kusa da daji kuma yana da nisan kilomita 35 zuwa garin Bukkuyum, headkwatar karamar hukumar. Yankin da wasu kauyuka masu yawa duk suna karkashin mulkin 'yan bindiga.

Mazauna yankin sun sanar da cewa sojojin kasa sun kafa bukkokinsu a yankin a cikin dajin. Sun ce 'yan ta'addan suna yawo a kan babura tare da wasu da ke yawo a kasa tare da shanunsu.

"Wani shugaban 'yan bindiga mai suna Shehu Bayade shi ke shugabantar ta'addancin, garkuwa da mutane da kuma satar shanu a yankunan Anka, Bukkuyum da Gummi a jihar," majiyar tace.
"Mun sakankance kan cewa Turji da yaransa sun samu gayyata ne daga Shehu Bayade zuwa dajin. A tunaninmu, yawan dajin ne yasa suka dawo sabooda jiragen NAF za su sha wuya kafin su gano inda suke.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

“Muna cikin babbar matsala. Muna rokon sojin da sauran hukumomin tsaro da su gangaro nan domin kuwa ba mu cikin kwanciyar hankali saboda dawowar mutanen nan ya kawo mana rashin natsuwa," yace.

Har a yayin rubuta wannan rahoton ba a samu zantawa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ba.

Bayan neman sulhu, shugaban 'yan bindiga,Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su

A wani labari na daban, Bello Turji, gagararren dan bindigan jihar Zamfara, a ranar Litinin ya sako mutane 52 wadanda suka dade a hannunsa, wata majiya ta tabbatar wa da Daily Trust hakan.

"Wadanda aka sako din a halin yanzu ana fito da su daga daji zuwa wani wuri da aka yi yarjejeniya inda daga nan za a kai su garin Shinkafi.
"Motoci sun yi layi kuma an umarce su da su fara tafiya hanyar Maberiya, wani yanki da ke da nisan kilomita 5 daga gabashin garin Shinkafi," wani mazaunin yankin da ya bukaci a bye sunansa ya sanar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

Asali: Legit.ng

Online view pixel