Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati

Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati

  • Malaman makaranta da iyayen yara sun nuna rashin jin dadinsu tare da sukar sabon salon aikin kwanaki 4 na makarantun gwamnati da El-Rufai ya kawo
  • Kamar yadda iyayen dalibai suka yi tsokaci, sun ce dama tabarbarewar karatun makarantun gwamnati ya yi yawa, wannan salo ne na nakasa karatun dan talaka
  • Malamai sun koka da yadda ake so su hade karatun kwanaki biyar cikin kwanaki hudu kuma ana tsammanin dalibai su fahimci inda aka dosa

Zaria, Kaduna - A ranar Litinin, 10 ga watan Janairu ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa malaman makarantun gwamnati za su dinga aikin kwanaki 4 kacal a cikin mako.

Legit.ng ta ruwaito muku yadda gwamnan ya bayar da sanarwar ga dukkan makarantun gwamnati na fadin jihar.

Sai dai wannan sanarwa ta janyo martani daban-daban daga malamai da kuma iyayen yara a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kaduna: El-Rufai ya ba da umarni ga makarantun gwamnati a koma karatun kwana 4

Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati
Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Legit.ng ta tattauna da wasu daga cikin iyayen da malaman inda mafi rinjaye suka nuna cewa wannan tsarin sam bai yi musu dadi ba kuma basu maraba da shi.

Wani mahaifin dalibi mai suna Malam Usman Hassan wanda ke kan hanyarsa ta kai dansa makarantar firamaren Baba Ahmed da ke Tudun Wada, Zaria, ya bayyana cewa ko kusa bai yi maraba da sabon tsarin ba.

A cewar Malam Usman:

"A gaskiya wannan sabon tsarin bai yi ba. Ta yaya za a ce yara su samu hutun har kwana 3 a mako daya? Me suke zama gidan su yi mana in baya da bari-bari?
"Sannan kowa ya san yadda karatun makarantun gwamnati suke a wannan zamanin. Ta yaya ake so a samu ilimin da ba a samu ba cikin kwanaki biyar a cikin kwanaki hudu."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan watanni 6, an sako daliban kwalejin da aka sace a Kebbi

Malam Usman ya yi kira ga gwamnatin Malam Nasir El-Rufai da ta sake duba tsarin nan, ta duba talaka kada ta yi ganganci bada gudumawa wurin tabarbara ilimin 'ya'yansu.

Wata malamar makaranta mai koyarwa a firamaren Turaki Ali da ke anguwan Magajiya a cikin garin Zaria, wacce ta nemi a boye sunanta, ta ce kwata-kwata bata ji dadin wannan sauyin ba.

Kamar yadda malamar ta sanar, ta na koyar da yara kuma suna fama inda da kyar ake samu cikin kwanaki biyar na mako su yi abinda ya dace.

"A gaskiya wannan sauyin bai yi mana dadi ba. Aikin kwanaki 5 ake so mu hade a kwanaki hudu, ta yaya yaran da da kyar suke daukan karatu a cikin kwana biyar ake ganin cire kwana daya zai amfane su?
"Komai da gwamnati za ta yi balle a fannin ilimi, ya dace ta duba abinda zai iya kaiwa da kawowa musamman a kan daliban. Wannan tsarin bai yi mana dadi ba. Ba wai bamu son hutu bane a matsayinmu na malamai, dalibanmu ne muke fara dubawa kuma su muke bai wa fifiko.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

"Baya ga nan, muna fatan ba wata makarkashiya bace gwamnatin ta hada wurin kokarin zabtare mana albashinmu ba," Malamar makarantar tace.

Kaduna: El-Rufai ya ba da umarni ga makarantun gwamnati a koma karatun kwana 4

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta umurci dukkan makarantun gwamnati da su koma aikin kwanaki hudu a mako, yayin da za a bude makarantun a ranar 10 ga watan Janairu a zango na biyu na shekarar 2021/2022.

Kwamishiniyar Ilimi, Halima Lawal, ta ba da wannan umarni ne a Kaduna ranar Lahadi a cikin sanarwar dawowa karatu a zango na biyu na shekarar 2021/2022, Daily Nigerian ta rahoto.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya nakalto cewa, gwamnatin jihar Kaduna a ranar 1 ga Disamba, 2021, ta sauya tsarin aiki zuwa kwanaki hudu mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel