Gayyatar Kukah daga DSS: Matasan Kiristoci sun koka, sun ce a gayyaci Sheikh Gumi

Gayyatar Kukah daga DSS: Matasan Kiristoci sun koka, sun ce a gayyaci Sheikh Gumi

  • Matasan kungiyar Kiristoci ta Najeriya, YOWICAN, ta caccaki hukumar tsaro ta farin kaya kan gayyatar Rabaren Kukah da suka yi
  • Matasan Kiristocin sun ce ya fi dacewa a gayyaci Sheikh Gumi, fitaccen malamin Musulunci, kan yadda ya ke ta'ammali da 'yan bindiga
  • A cewa, YOWICAN, za su wakilci Rabaren Kukah na Sakwato wurin amsa gayyatar, amma a gayyata mai bin 'yan bindiga har daji

Sakwato - Wasu matasan Kiristoci karkashin jagoranci kungiyar Kiristocin Najeriya, reshen matasa, YOWICAN, a ranar lahadi sun yi suka game da gayyatar faston cocin katolika na jihar Sakkwato, Rabaren Mathew Kukah, wanda hukumar tsaro ta farin kaya, SSS tayi.

Daily Nigerian ta tattaro yadda SSS ta gayyaci Kukah sanadiyyar furucinsa akan halin da kasa ke ciki inda yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Gayyatar Kukah daga DSS: Matasan Kiristoci sun koka, sun ce a gayyaci Sheikh Gumi
Gayyatar Kukah daga DSS: Matasan Kiristoci sun koka, sun ce a gayyaci Sheikh Gumi. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Yayin mayar da martani, shugaban YOWICAN, Belusochukwu Enwere, a wata takarda da ya fita ranar Lahadi, ya ce sai dai hukumar ta gayyaci sanannen malamin addinin Musuluncin nan, Ahmed Gumi, domin ya amsa tambayoyi akan nuna kauna ga 'yan bindiga.

Kamar yadda takarda tace:

"Hankalin YOWICAN ya dawo ne bayan sakon gayyatar da aka kai wa malamin addinin Kirista Fasto Hassan Kukah. Faston bai aikata wani laifi ba, gwamnati ta mayar da hankalin ta gurin yakar 'yan bindiga da 'yan ta'adda.
"Cikin kwanakin nan, sama da mutane 200 suka rasa rayukansu a jihar Zamfara da kauyukan kusa. Tabbas wannan abun alhini ne. Za mu shirya dukkan matasan Kiristocin fadin kasar nan dan girmama wannan gayyatar.
"DSS ta mika gayyatar ta ne garemu, ba Fasto Kukah ba kadai, kuma za mu girmama gayyatar. DSS ta fara gayyatar Ahmad Gumi dan ya amsa tambayoyi na hada kai da 'yan bindiga da yake.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An kashe 'yan Boko Haram 950, 24,059 sun mika wuya a kasa da watanni 7

"Fitaccen malamin addinin Musuluncin da ya dade yana kawo cece kuce, Ahmad Gumi, ya shawarci mutane a yankunan da 'yan ta'adda suka fi kai hari, Arewa-maso yammacin kasar Najeriya akan yadda za su rayu cikin kwanciyar hankali tare da 'yan ta'adda a dajikansu," inji kungiyar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, YOWICAN ta yanko daidai inda Gumi yake cewa mutane zasu iya samar da "fahimtar juna da 'yan bindiga ba tare da sun cutar dasu ba".

A cewar Enwere, Gumi ya dade yana "nuna kauna ga 'yan bindiga kuma yana zaune lafiya ba tare da wani gayyata daga DSS ko 'yan sanda ba".

Yace:

"DSS sun gayyaci Fasto Mathew Kukah ne dan ya amsa tambayoyi, wasu kwanaki bayan ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari wankin babban bargo na gazawa wurin bada tsaro a fadin kasar.
"Fasto Kukah ya soki Buhari ne a wa'azin da ya gabatar na Kirsimeti, inda yace shugaban Najeriya ya gaza nuna bajintarsa yayin da 'yan ta'adda, 'yan bindiga da sauran hatsabibai suka mamaye fadin kasar."

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

JNI ta zargi Kukah da jifan Musulmi da 'kibiya mai matukar dafi'

A wani labari na daban, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya jagoranci JNI a ranar Laraba inda suka yi wa shugaban addinin Kirista na yankin jihar Sokoto, Bishop Matthew Kuka, wankin babban bargo akan taron da ya shirya a ranar Kirsimeti.

Kungiyar ta kwatanta taron Kirsimetin da Kukah ya tattara a matsayin kibiya mai dafi da ya harba ga Musulunci da Musulman kasar Najeriya, The Cable ta ruwaito.

A wata takardar JNI da suka saki bayan makonni 3 da Bishop din ya tura wani sako ga shugaba Muhammadu Buhari, wanda yake zarginsa da son kai da wariya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel