Nasara daga Allah: An kashe 'yan Boko Haram 950, 24,059 sun mika wuya a kasa da watanni 7

Nasara daga Allah: An kashe 'yan Boko Haram 950, 24,059 sun mika wuya a kasa da watanni 7

  • Hukumar tsaro a Najeriya ta bayyana adadin 'yan ta'addan da ta hallaka a cikin watanni bakwai na shekarar da ta gabata
  • Wannan na zuwa ne yayin da rundunar sojin Najeriya ke ci gaba da aikin ragargazar 'yan ta'adda a Arewacin kasar nan
  • Rahoton na soji ya bayyana irin aikin da rundunar sojin Najeriya ta yi a cikin wannan kankanin lokaci

Abuja - Dakarun Operation Hadin Kai, sun kawar da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 950 a yankin Arewa maso Gabas tsakanin 20 ga Mayu, 2021 zuwa 6 ga Janairu, 2022, kamar yadda hedkwatar tsaro ta bayyana, Daily Nigerian ta rahoto.

Mukaddashin Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka a lokacin da yake bitar yadda ayyukan suke gudana a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

Mai magana da yawun soji
An hallaka 'yan Boko Haram 950, 24000 sun mika wuya a kasa da watanni 7 | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Mista Onyeuko ya ce sojojin sun kawar da wasu manyan kwamandoji da kuma shugabannin kungiyoyin ta’addanci a lokacin.

Jaridar The Cable ta rahoto Onyeuko na cewa, ya zuwa yanzu ‘yan ta’adda 24,059 da iyalansu da suka hada da manya maza 5,326, manya mata 7,550 da kananan yara 11,183 ne suka mika wuya ga sojoji a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin ya ce an dauki bayanan duk wasu da suka mika wuya yadda ya kamata tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar matakan da suka dace.

Mista Onyeuko ya kara da cewa an kama ‘yan ta’adda 79 yayin da aka ceto mutane 113 da aka yi garkuwa dasu a cikin wannan lokaci.

Ya kara da cewa:

“Hakazalika, an kwato makamai iri-iri 195 da suka hada da bindigogin AK-47, GPMGs, bindigogin PKT da kuma bindigu na gida daga hannun ‘yan ta’adda a yayin gudanar da aikin.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

“Bugu da kari, an kwato jimillar alburusai iri-iri 2,385 da kuma dawo da dabbobi sata 253.
“Hakazalika, an lalata motocin ‘yan ta’addan guda 14 a yayin da ake gudanar da aikin, yayin da sojoji suka kwato motocin bindigogi 16 a wannan lokacin."

'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

Daruruwan mazauna kauyuka biyar ne a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum na jihar Zamfara suke ta tururuwa zuwa cikin garin Anka bayan da ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama a kauyukansu.

Majiyoyi da suka zanta da jaridar Premium Times sun ce har yanzu ba a tantance adadin wadanda aka kashe ba.

Wani lauya wanda kuma mamba ne a kungiyar agaji ta Zamfara, ya ce ya ga yawancin mutanen kauyen da suka rasa matsugunai a sakateriyar karamar hukumar Anka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel