Mutuwa rigar kowa: Wata Amarya ta rasu kwanaki kaɗan bayan shigarta dakin mijinta a Kano

Mutuwa rigar kowa: Wata Amarya ta rasu kwanaki kaɗan bayan shigarta dakin mijinta a Kano

  • Allah mai yadda ya so kuma a lokacin da ya so, wata Amarya ta koma ga Ubangijinta kwanaki kaɗan bayan ɗaura mata aure
  • Fatima Balarabe, ta rasu ne bayan wata daya da kwana biyar da fara rayuwar aurenta, wanda aka ɗaura a watan Disamba, 2021
  • Mahaifinta, Balarabe A. Haruna, ya yi godiya ga Allah bisa ni'imar da ya masa na ba shi ɗiya kamar Fatima, tare da addu'ar Allah ya jikanta

Kano - Wata Amarya mai suna, Fatima Balarabe Haruna, ta riga mu gidan gaskiya ƙwanaki 35 da fara sabuwar rayuwar aure a ɗakin mijinta a jihar Kano

Mahaifin marigayya Fatima, Balarabe A Haruna, shi ne ya sanar da rasuwar diyarsa a dandalin sada zumunta Facebook.

Yace an ɗaura auren Fatima Balarabe a ranar 4 ga watan Disamba, 2021, wata ɗaya da kwana biyar kenan kuma Allah ya karbi abinsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kamaru ta lallasa Burkina Faso a wasan farko na gasar AFCON 2021

Fatima Balarabe
Mutuwa rigar kowa: Wata Amarya ta rasu kwanaki kaɗan bayan shigarta dakin mijinta a Kano Hoto: Balarabe A. Haruna
Asali: Facebook

Malam Balarabe ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya bashi ikon tarbiyyantar da ita, har ta girma kuma ya aurar da ita.

Yace:

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, an haifi Maryam Balarabe ranar 8 ga watan Agusta, 1999, kuma ta yi aure ranar 4 ga watan Disamba, 2021, kuma ta koma ga mahaliccin ta ranar Lahadi 9 ga watan Janairu, 2021.
"Muna godiya ga Allah da ya bamu ita, ya taimaka mana muka tarbiyyantar da ita ta girma, muka bata ilimi, da kuma kasancewarta cikin mu, muna ƙara gode masa."

Menene sanadin rasuwarta?

A cewar mahaifinta, Fatima ta rasu ne bayan fama da yar gajeruwar rashin lafiya, wata ɗaya da kwana 5 da ɗaura aurenta.

Ya kuma mika godiyarsa ga yan uwa da abokan arziki, waɗan da suka taimaka yayin rashin lafiyarta da kuma waɗan da suka halarci Jana'iza.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta

"Ina rokon Allah ya yafe mata kurakuranta, ya jikanta da rahama, ya ɗaukaka darajarta, ya kuma saka mata da gidan Ajannatul Firdausy."
"Ina godiya ga dukkan waɗan da suka zo wurin Addu'ar ɗiya ta ta farko kuma ɗaya tilo, domin ta samu rahamar Allah, kuma ta haɗu da bayin Allah nagari a lahira."

A wani labarin na daban kuma Wani mummunan hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 19 a jihar Kano

Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Kano tace wani mummunan hatsari ya lakume rayukan aƙalla mutum 19.

Kwamandan FRSC na jihar Kano, Mato Zubairu, yace wasu motoci biyu ɗauke da mutum 45 ne suka yi taho mu gama a Bebeji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel