Innalillahi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta

Innalillahi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta

  • Rahoton da ke iso mu ya bayyana cewa, diyar sarkin Ogbomoso, Farfesa Taibat Danmole ta riga mu gidan gaskiya
  • Kwanaki 28 da suka gabata ne mahaifinta, Oba Oladunni Oyewumi ya yi sallama da duniya bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Majiya ta bayyana lokacin da za a yi jana'izar wannan baiwar Allah kamar yadda addini ya koyar

Jihar Kwara - Mutuwa ta sake sallama a gidan marigayi Soun na Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewumi a jihar Kwara.

Oba Oyewumi ya rasu ne a ranar 12 ga watan Disamba yana da shekaru 95, inda aka tattaro cewa diyar marigayi sarkin, Farfesa Taibat Danmole ta rasu a ranar Asabar 8 ga watan Janairu tana da shekaru 71 a duniya.

Wasu majiyoyi a fadar sun shaida wa jaridar Punch a ranar Lahadi cewa Danmole ta dade tana jinya kafin ta rasu ranar Asabar, kwanaki 28 bayan da mahaifinta ya yi sallama da duniya.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Mutuwa a gidan sarautar Ogbomosho
Da dumi-dumi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta | Hoto: naijanews.com
Asali: Facebook

Daya daga cikin majiyoyi ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“'Yar fari ga Baba ta rasu. Ta jima tana jinya kuma jiya ne hakan ya faru. Muna addu’ar Allah ya ja kwanakin wadanda suka rage mana.”

Danmole, wanda aka haifa a ranar 19 ga Maris, 1951, an tattaro cewa, za a yi jana’izarsa a ranar Lahadi da rana a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Marigayiyar, wacce aka ce Farfesa ce a fannin ilimi, ta auri wani malamin jami’a, Farfesa Hakeem Danmole, wanda shi ne shugaban kwalejin nazarin al’umma da kimiyar zamantakewa a jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin.

Ta kasance kwamishiniyar ilimi a jihar Oyo daga 1997-1998. Ta kasance memba, Panel Visitation to The Polytechnic na Ibadan a 2011.

Rasuwar mahaifinta

A bangare guda, basaraken garjiya mai sarautar Soun na Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewumi, Ajagungbade III, ya rasu.

Kara karanta wannan

Babban taro: Gwamnonin APC za su gana da Shugaba Buhari don tsayar da rana

Majiyoyi na kusa da sarkin a fadar sun shaida wa wakilin jaridar Punch cewa, basaraken mai shekaru 95 ya rasu ne da safiyar yau Lahadi.

Wasu majiyoyi guda biyu ne suka tabbatar da hakan a garin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewar majiyar:

“Gaskiya ne Baba ya rasu. Hakan ya faru da safiyar yau amma ba a sanar da hakan a hukumance ba.
“Ya yi rayuwa mai kyau kuma ya bar suna mai kyau da yawa. Nan ba da jimawa ba fadar za ta sanar da hakan.”

A wani labarin daban, Allah ya yi wa Olubadan na kasar Ibadan, Oba Saliu Adetunji rasuwa.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 93 a duniya. Jaridar Punch ta tattaro cewa sarkin ya rasu ne a asibitin kwalejin jami’a dake Ibadan a jihar Oyo.

Majiyoyin fadar sun tabbatar da mutuwarsa, amma sun nemi a sakaya sunayensu.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Ku hakura ku bar mun - Mustapha ya roki Almakura, Yari, Sheriff da sauransu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel