Da Dumi-Dumi: Kamaru ta lallasa Burkina Faso a wasan farko na gasar AFCON 2021

Da Dumi-Dumi: Kamaru ta lallasa Burkina Faso a wasan farko na gasar AFCON 2021

  • Mai masaukin baki, Kamaru, ta bude wasan kwallon kafa na gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON 2021
  • Tawagar yan wasan Kamaru sun samu nasara kan Burkina Faso da ci 2-1, a fafatawar da suka yi ranar Lahadi
  • Gasar wacce ya kamata a yi a 2021, hukumomi sun dage ta ne saboda ɓarkewar cutar COVID19

Cameroon - Tawagar kungiyar kasar Kamaru, mai masaukin baki, ta buɗe gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka (AFCON) inda ta fafata da Burkina Faso a wasan farko na rukunin A, ranar Lahadi.

Punch ta rahoto cewa tawagar Kamaru ta yi bajinta yayin da yunkuro har ta samu nasara da ci 2-1 a wasan da suka fafata a filin Olembe Stadium, dake Yaoundé.

Ɗan wasan Burkina Faso, Sangare, shine ya fara jefa kwallo a ragar Kamaru, a minti na 24 da fara wasa, kwallon da ta kasance ta farko a AFCON na bana.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa uwargidar Janar Buba Marwa, Mrs Zainab, rasuwa

Afcon
Da Dumi-Dumi: Kamaru ta lallasa Burkina Faso a wasan farko na gasar AFCON 2021 Hoto: AFCON 2022
Asali: Facebook

A minti na 40 da fara wasa, ɗan wasan gaba na Kamaru, Vincent Aboubakar, ya rama kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron raga wato Firanati.

Kazalika, Abubakar ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar Burkina Faso, a wani bugun daga kai sai mai tsaron raga da suka ƙara samu a cikin karin mintuna na kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Wannan shi ne wasa na uku da ƙasashen biyu suka fafata da juna a gasar AFCON, kuma duka sauran biyun sun kasance a wasan rukuni.

Kamaru ta samu nasara kan Burkina Faso a haɗuwarsu ta farko a shekarar 1998, kafin kuma su raba maki da ci 1-1 a shekarar 2017.

Wannan ne karo na 20 da Kamaru ta halarci gasar AFCON, inda kasashen uku ne kacal suka sha gabanta a yawan halartan gasar.

Kara karanta wannan

Halifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tahir Bauchi, da manyan Maluma sun taru a Kano don addu'a

Ƙasar Kamaru na karban bakuncin AFCON karo na biyu a tarihi, shekara 50 bayan na farko a shekarar 1972, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Jerin kasashe 10 da Cristiano Ronaldo ya jefa wa kwallaye uku rigis a raga

Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa ɗan asalin kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya kafa sabon tarihi a fagen zura kwallo uku a wasa ɗaya

Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya zura kwallo uku rigis a wasa ɗaya yayin da yake wakiltar ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel