Wata sabuwa: 'Yan a daidaita sahu sun tsunduma yajin aiki a jihar Kano

Wata sabuwa: 'Yan a daidaita sahu sun tsunduma yajin aiki a jihar Kano

  • Matuka a daidaita sahu a jihar Kano sun ci alwashin fadawa yajin aiki a yau Litinin 10 ga watan Janairu
  • Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta zargi yadda gwamnati ke karbar haraji daga hannun masu sana'ar
  • Hakazalika, kungiyar ta yi gargadi ga mambobinta kan fitowa aiki yayin da aka shiga wannan yajin aikin

Jihar Kano - Kungiyar masu tuka a daidaita sahu ta jihar Kano ta bayyana kudurinta na fadawa yajin aiki daga yau Litinin 10 ga watan Janairu.

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta ga yadda ake tafiyar da sana'ar a daidaita sahu a jihar.

'Yan a daidaita sahu sun shiga yajin aiki a Kano
Wata sabuwa: 'Yan a daidaita sahu sun tsunduma yajin aiki a jihar Kano | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Hakazalika, kungiyar ta koka kan yadda ake cin mutuncin masu sana'ar a jihar, inda kuma ta koka kan yadda mambobinta ke biyan haraji ba kan gado.

Kara karanta wannan

KAROTO ga 'yan daidaita sahun da suka shiga yajin aiki: Za ku gane shayi ruwa ne

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar wacce wakilinmu a Legit.ng Hausa ya gani, kungiyar ta bayyana wani gargadi ga mambobinta, inda tace:

"Gargadi ga duk wani dan a daidaita sahu matukin a daidaita sahu na jahar Kano, idan ka sake ka fito aiki , to duk abin da ya faru da mashin dinka kai ka jawowa kanka. Saboda haka don Allah a bamu hadin kai."

Hakazalika, sanarwar ta yi kira ga mambobinta da su cire tsoro su kwaci kansu daga halin da suke ciki a yanzu a jihar.

Ba wannan ne karon farko da kungiyar za ta shiga yajin aiki ba, a shekarar 2021 sun yi yajin aikin da ya jawo cece-kuce a jihar.

Ya taba faruwa a Borno

A wani labarin, fasinjoji sun tattaru da safiyar Litinin a Minna, jihar Neja bayan direbobin napep sun shiga yajin aikin gargaɗi na yini ɗaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Fusatattun masu napep sun toshe hanyar Shiroro da shataletalen Mobil yayin da suke tilastawa duk wani dan napep ya tsaya, sannan su sallami fasinjan da ya dauko, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Masu napep din sun dauki wannan matakin ne domin nuna fushinsu kan yadda yan sanda, jami'an kare hadurra, VIO, da masu karbar haraji suke matsa musu a yankin Chanchaga da Bosso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel