Fusatattun Direbobin Keke Nafef Sun Shiga Yajin aiki, Sun Toshe Hanyoyi a Jihar Arewa

Fusatattun Direbobin Keke Nafef Sun Shiga Yajin aiki, Sun Toshe Hanyoyi a Jihar Arewa

  • Masu keke nafef sun tsunduna yajin aikin gargaɗi a Minna, jihar Neja bisa matsin lambar da hukumomi ke musu
  • Direbobin sun ce suna shan matsin lamba daga yan sanda, jami'an amsar haraji, jami'an VIO da sauransu
  • Rahoto ya nuna cewa fasinjoji da dama sun tattaru yayin da masu yajin aikin suka toshe manyan hanyoyi

Niger - Fasinjoji sun tattaru da safiyar Litinin a Minna, jihar Neja bayan direbobin nafef sun shiga yajin aikin gargaɗi na yini ɗaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Fusatattun masu nafef sun toshe hanyar Shiroro da shataletalen Mobil yayin da suke tilastawa duk wani ɗan nafef ya tsaya, sannan su sallami fasinjan da ya ɗakko, kamar yadda punch ta ruwaito.

Masu nafef ɗin sun ɗauki wannan matakin ne domin nuna fushinsu kan yadda yan sanda, jami'an kare haɗurra, VIO, da masu karbar haraji suke matsa musu a yankin Chanchaga da Bosso.

Kara karanta wannan

Hotunan Gidan da Aka Tsinci Gawar Babban Ɗan Sanatan APC a Kaduna

Derebobin Nafef sun shiga yajin aiki a Minna
Fusatattun Direbobin Keke Nafef Sun Shiga Yajin aiki, Sun Toshe Hanyoyi a Jihar Arewa Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin direbobin Nafef yace:

"Banda matsin lamba da tsadar da jami'an amsar haraji suke mana a Chanchaga da Bosso kan dole sai mun rubuta lambar rijista a jikin keken mu da girma, wanda muke ganin zai lalata mana keke."
"Yan sanda, jami'an hukumar kare haɗurra, da jami'an VIO suna matsa mana a kowace rana. Idan suka kama mutum suka tafi da shi ofishinsu dole sai ya biya N5,000 kafin su sake shi, abin ya yi yawa."

Zamu cigaba da yajin aiki har sai an biya mana bukatun mu

Wani direban nafef, Junaidu Abubakar, yace zasu cigaba da wannan yajin aikin matukar hukumomi suka gaza warware matsalolin su musamman abinda yan sanda da sauran hukumomin tsaro ke musu.

Ma ajiyin kungiyan masu nafef reshen jihar, Suleiman Danjuma, yace basu da masaniya, sun tashi da safe sun ga mambobin sun ɗauki wannan matakin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

Danjuma yace:

"Yajin aikin yana da alaƙa da yawan harajin da gwamnati ke karba, da yawan kame da jami'an VIO suke wa direbobin kan lamarin lambar rijista a karamar hukumar Chanchaga."
"Ba wai suna adawa da rijistar bane amma yanda ake cewa su rubuta lambar a jikin keke yana bata musu abun sana'ar ta su."

Fasinjojin Nafef sun shiga matsanancin hali

Wasu fasinjoji da suka zo daga wajen garin Minna ba tare da sanin abinda ke faruwa ba lamarin ya ritsa da su.

Wata mata, Aisha, wanda ta fito daga Paiko, ta shigo Minna domin siyan kayan abinci ta roki yan nafef da hukumomi su sasanta kansu domin talakawa su samu damar yin harkokin gaban su.

Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ci tura.

A wani labarin kuma 'Diyar Wani Jami'in Tsaro Ta Kai Karar Mahaifinta Bisa Keta Mata Haddi Na Tsawon Shekaru a Kano

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Dakarun Sojoji Sun Yi Artabu da Mayakan Boko Haram a Yobe

Hukumar kare hakkin ɗan adam ta kasa ta fara bincike kan korafin da aka shigar mata na wani mahifin mata uku.

Ɗaya daga cikin ƴaƴansa ne ta kai rahoton cin mutunci da keta haddin da mahaifinsu ke musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel