KAROTO ga 'yan daidaita sahun da suka shiga yajin aiki: Za ku gane shayi ruwa ne

KAROTO ga 'yan daidaita sahun da suka shiga yajin aiki: Za ku gane shayi ruwa ne

  • Hukumar KAROTA a jihar Kano ta yi martani mai zafi kan yadda kungiyar matuka a daidaita sahu suka shiga yajin aiki
  • Hukumar ta ce, sam hakan ba daidai bane, kuma ba zai haifarwa direbobin da mai ido ba, saboda wasu dalilai
  • Hakazalika, hukumar ta ce, rashin fitowar direbobin a daidaita sahu a fadin Kano ya sa jihar ta samu salama wajen bin dokar tuki

Jihar Kano - Jim kadan bayan da kungiyar direbobin a daidaita sahu ta sanar da tsundumawa yajin aiki a jihar Kano, KAROTA ta yi martani mai zafi, inda ta nuna bacin ranta ga yadda lamarin yajin ya kasance.

Shugaban KAROTA Baffa Babba Danagundi ne yayi martani kan yajin aikin a ranar Litinin 10 ga watan Janairu, kasa da sa'o'i 24 da shiga yajin aikin.

KAROTA ta yi martani kan tafiya yajin aikin 'yan a daidaita sahu
Martanin 'yan KAROTO ga direbobin a daidaita sahu: Za ku gane shayi ruwa ne | Hoto: freedomradionig.com
Asali: UGC

Gidan radiyon Freedom ya bayyana cewa, Baffa ya bayyana a shirin Barka da Hantsi na gidan radiyon, inda ya yi martani da cewa, lallai matuka a daidaita sahu za su gane shayi ruwa ne.

Ya ci gaba da cewa, wannan yajin aiki ƙilu ce za ta jawo bau ga masu adaidaitar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa, shiga yajin aikin ba zai haifar da mai ido ba, domin kuwa zai sake tado da wasu sabbin abubuwa ne, inda yace rashin fitowarsu ya sa ana bin ka'idojin tuki a jihar.

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo rahoton yadda kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta ga yadda take biyan haraji ba gaira ba dalili.

A bangaren KAROTA, ta sha bayyana matsayarta da cewa, tana nan daram, kuma gyara take kokarin kawo wa a jihar, musamman a fannin sufuri.

A bangaren mazauna jihar Kano, Daily Trust ta rahoto yadda mazauna suka shiga matsi, inda ababen hawa suka yi wahalar samu a wasu yankunan.

'Yan a daidaita sahu sun tsunduma yajin aiki a jihar Kano

A tun farko, kungiyar masu tuka a daidaita sahu ta jihar Kano ta bayyana kudurinta na fadawa yajin aiki daga yau Litinin 10 ga watan Janairu.

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta ga yadda ake tafiyar da sana'ar a daidaita sahu a jihar.

Hakazalika, kungiyar ta koka kan yadda ake cin mutuncin masu sana'ar a jihar, inda kuma ta koka kan yadda mambobinta ke biyan haraji ba kan gado.

Asali: Legit.ng

Online view pixel