Rashin tsaro: Jerin farmaki 5 da suka tada hankalin 'yan arewa a 2021

Rashin tsaro: Jerin farmaki 5 da suka tada hankalin 'yan arewa a 2021

  • Rashin tsaron Najeriya ya kazanta a shekarar 2021 yayin da kasar ta fuskanci miyagun farmaki a tarihin kasar
  • Kusan dukkan sassan kasar Najeriya sun yi fama da miyagun farmaki wadanda suka hada da Boko Haram/ISWAP, 'yan bindiga ko kuma 'yan aware
  • Hakazalika, kasar Najeriya ta fuskanci ibtila'in sace yara 'yan makaranta tare da yin garkuwa da su a cikin shekarar da ta gabata

Shekarar 2021 ta kasance ba mai sauki ba ga 'yan Najeriya sakamakon munanan ayyukan 'yan bindiga da 'yan ta'addan Boko Haram.

A cikin rashin kyautawar 'yan ta'addan da miyagun al'amuran da suka aiwatar a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, sun gigita yankunan inda ake ganin cewa babu yankunan da aka zubda jini kamar nan.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a Jos yayin da aka sake tsintar gawar wata mace babu idanu da wasu sassa na jikinta

Rashin tsaro: Jerin farmaki 5 da suka tada hankalin 'yan arewa a 2021
Rashin tsaro: Jerin farmaki 5 da suka tada hankalin 'yan arewa a 2021. Hoto daga thenationonline.ng
Asali: UGC

Sai dai kuma, mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a koyaushe ya na ikirarin cewa 'yan Najeriya sun fi samun tsaro a karkashin gwamnatin fiye da gwamnatocin baya.

Ga wasu biyar cikin miyagun farmakin da arewacin kasar nan ya fuskanta a 2021 kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

1. Satar daliban jami'ar Greenfield

A watan Afirilun shekarar da ta gabata, 'yan ta'adda sun kutsa jami'a mai zaman kanta ta Greenfield da ke jihar Kaduna inda suka sace dalibai masu tarin yawa.

2. Satar yaran makarantar Bethel Baptist

A sa'o'in farko na ranar 5 ga watan Yulin shekarar da ta gabata, 'yan ta'adda sun kutsa makarantar da ke Maraban Damishi a Kujama da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka tasa keyar dalibai 12.

Kara karanta wannan

Umarnin IPOB: Za mu kaurace wa kayayyakin kudu, CNG ta ja kunne

3. Satar yaran makarantar Kagara

A watan Fabrairu, 'yan ta'adda sun kutsa makarantar sakandaren gwamnati da ke Kagara a jihar Niger inda suka sace mutum 42, 27 daga cikin dalibai ne, malamai 3 da wasu iyalai 12.

4. Satar daliban FGC Yauri

'Yan ta'adda dauke da miyagun makamai a watan Yuni sun sace malamai 2 da dalibai talatin na kwalejin gwamnatin tarayya da ke Yauri a jihar Kebbi, arewa maso yammacin Najeriya.

5. Kone fasinjoji a Sokoto

Miyagun 'yan ta'adda cike da rashin imani da tausayi a watan Disamban shekarar da ta gabata sun kone fasinjoji arba'in da ransu da ke kokarin yin gudun hijira a jihar Sokoto.

Bayan kwashe wata 7 a hannun ƴan ta'adda, ɗaliɓan FGC Kebbi sun shaƙi iskar ƴanci

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kebbi ta ce an sako dalibai 30 da malami daya na kwalejin gwamnatin tarayya (FGC) Birnin Yawuri wadanda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Neman zaman lafiya: Shugaba Buhari ya jaddada kudurinsa na samar burtali ga Fulani

Yahaya Sarki, hadimin gwamna Atiku Bagudu ne ya tabbatar da nasarar a ranar Asabar, TheCable ta ruwaito.

A watan Yunin 2021, wasu ‘yan bindiga sun afka makarantar inda su ka yi garkuwa da dalibai da dama da malamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel