Umarnin IPOB: Za mu kaurace wa kayayyakin kudu, CNG ta ja kunne

Umarnin IPOB: Za mu kaurace wa kayayyakin kudu, CNG ta ja kunne

  • Kungiyoyin hadin guiwa na Arewa, CNG, ta yi kira ga 'yan arewa kan su kaurace wa dukkan kayayyaki da kasuwancin Ibo a arewa
  • Kungiyar ta sanar da hakan ne a matsayin martani da kuma matakin da za ta dauka kan haramta cin naman shanun Fulani da IPOB ta yi
  • Kungiyar ta yi kira ga 'yan arewa da su kaurace wa dukkan wasu kungiyoyin siyasa da dukkan 'yan siyasan kudancin kasar nan

Kungiyoyin hadin guiwa na arewa, CNG, ta yi barazanar kauracewa dukkan kasuwanci da Ibo ke yi a fadin arewacin Najeriya.

CNG ta bayar da wannan jan kunnen ne a matsayin martani kan haramta amfani da shanun Fulani da 'yan awaren IPOB suka yi, Daily Trust ta ruwaito.

Umarnin IPOB: Za mu kaurace wa kayayyakin kudu, CNG ta ja kunne
Umarnin IPOB: Za mu kaurace wa kayayyakin kudu, CNG ta ja kunne. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda da IPOB ta fitar ranar Asabar, wadanda suke ta saka dokar hana fita a kudu maso gabas, sun umarci mutanen yankin da su daina cin naman shanun da aka kai yankin daga arewa daga ranar 8 ga watan Afirilun 2022.

Kara karanta wannan

Hana cin nama daga Arewa: Kungiyar masu safarar abinci da shanu sun mayar wa IPOB zazzafan martani

"Ranar 8 ga watan Afirilun 2022 ne ranar. Daga ranar, babu wani shanun Fulani da za a sake bari ya shiga kasar Biafra kan kowanne dalili, birniya, nadin sarauta, biki da sauransu," takardar tace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma CNG ta bakin kakakinta, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce tabbas wannan sanarwa ta fusata su kuma babbar barazana ce ga kasuwancin arewa a kudu maso gabas da kuma 'yan arewa da ke zama a yankunan Ibo.

"A kokarin ganin an shawo kan duk wata barazana kai tsaye ko a kaikaice ga 'yan arewa a ko ina a kasar nan, CNG na kira kan kauracewa dukkan kasuwan, kayayyaki da Ibo ke siyarwa a watan Afirilu.
“CNG ta yi kira ga 'yan arewa da ke ko ina da su daina nuna goyon baya ga jam'iyyar siyasa da kungiyoyi da ke kudu maso gabas tare da 'yan siyasar su.

Kara karanta wannan

Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari

“Domin kore shakka, arewa yayin kiyaye al'adarta ta hakuri da juriya, ba za ta cigaba da lamintar kowanne irin barazana da hantara ba da aka yi domin dakile halastattun kasuwancin 'yan arewa a kowanne sashi na kasar nan."

Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kare gwamnatinsa kan hukuncinta na karbo basussuka daga China, ya ce duk wanda zai taimaka wurin samarwa da Najeriya ababen more rayuwa ana maraba da shi.

Kamar yadda bayanin da Ofishin kula da basussuka ya sanar, Najeriya ta aro $2.02 biliyan a matsayin bashi daga China daga 2015 kuma bashin kasar nan ya kai $3.40 biliyan daga China a ranar 31 ga watan Maris na shekarar da ta gabata.

A yayin jawabi a tattaunawar da suka yi da Channels TV, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa duk lokacin da bukatar karbo bashi daga kasar waje ta taso, gwamnatinsa za ta yi hakan.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel