Dakarun sojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai, sun ceto mutane masu yawa

Dakarun sojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai, sun ceto mutane masu yawa

  • Luguden wutar da sojojin Najeriya ke yi wa 'yan bindiga a Zamfara ya tada musu hankali tun bayan da gwamnatin tarayya ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda
  • Duk da 'yan ta'addan sun dinga kashe mutane yayin da suke kan hanyarsu ta sauya sheka, alamu sun nuna cewa sun matukar gigicewa da ruwan wutan da soji ke musu
  • Sojoji, 'yan sanda da 'yan sa kai suna ta karbo wadanda miyagun suka yi garkuwa da su ba tare da an biya su kudin fansa ba sakamakon firgicin da suke ciki

Zamfara - Yayin da 'yan bindiga da suke kokarin tserewa daga luguden wutar sojoji suka ratsa kauyuka, jami'an tsaron sirri na sojoji sun yi ta kokarin amso wadanda aka yi garkuwa dasu daga shugabannin 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

PRNigeria ta tattaro yadda 'yan bindigan da suka riga suka firgita suka kai hari a yankunan Anka da Bukkuyum na jihar Zamfara, wasu shugabannin 'yan bindiga a Shinkafi da wuraren Tsafe sun turo da wakilansu ga hukumomi inda suke neman zaman lafiya tare da cigaba da sakin wadanda suka yi garkuwa da su.

Dakarun sojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai, sun ceto mutane masu yawa
Dakarun sojin Najeriya sun yi ruwan bama-bamai, sun ceto mutane masu yawa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

'Yan bindiga a jihar Zamfara a halin yanzu suna cikin firgici, sanadiyyar luguden wutar da sojojin Najeriya suke cigaba da yi musu bayan gwamnatin tarayya ta ayyana kungiyoyin 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.

Majiya daga hukumar tsaro ta bayyana wa PRNigeria yadda sojojin Najeriya suka kai farmaki ga sansaninsu kuma suka yi nasarar sheke wasu daga cikin shugabanninsu, yayin tserewa ne 'yan bingida suka kai hari kauyuka.

"Lokacin da suke kokarin tserewa daga mazauninsu tare da dabbobinsu sanadiyyar luguden wuta, 'yan bindiga sun bude wa 'yan sa kai wuta sannan suka kai farmaki kauyuka. Wasu daga cikin yankin da suka kai hari sun hada da Barayar Zaki, Rafin Geri, Rafin Danya da Kurfa.

Kara karanta wannan

Zamfara: An samo gawawwaki 143 yayin da aka cigaba da neman wasu

"'Yan ta'addan sun samu labarin yadda sojojin suke kokarin ragargazarsu. Cigaba da kai musu farmaki ya rage yawansu matuka, ta kai ga an yi nasarar sheke yanwancin shugabanninsu,"inji majiyar.

Kamar yadda majiyar ta bayyana,ayyana 'yan bindigan a matsayin 'yan ta'adda ya bayar da halascin yakarsu da shugabanninsu a Zamfara da sauran jihohin Arewa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Bayan gane aibun ayyana 'yan bindigan a matsayin 'yan ta'adda da gwamnatin tarayya tayi, wasu shugabanninsu sun saki tarin mutanen da suka yi garkuwa da su a Shinkafi, Tsafe da wuraren Kaura har da neman sulhu.

Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji

A wani labari na daban, Bello Turji, gagararren dan bindigan da ya addabi yankin arewa maso yamma, ya sauya sheka daga jihar Zamfara sakamakon tsananin luguden wutar da sojojin Najeriya ke yi musu.

Daily Trust ta ruwaito yadda sojojin saman Najeriya suka ragargaza sansanonin 'yan bindiga a samamen da suke ta kaiwa yankin.

Kara karanta wannan

Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, gagararen dan bindigan da mutanensa sun hanzarta barin dajin da suke saboda jiragen NAF suna ta ragargazar dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi kuma suna tafiya kudancin Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel