Yadda Gwamna Zulum ya tallafawa sojoji ba tare da sun roke shi ba, Shugaban dakarun soji

Yadda Gwamna Zulum ya tallafawa sojoji ba tare da sun roke shi ba, Shugaban dakarun soji

  • Mukaddashin kwamandan rundunar soji ta 7 dake yaƙi da Boko Haram, ya bayyana taimakon da Zulum ya yi wa sojoji ba tare da nema ba
  • Manjo Janar A.A. Eyitayo, yace da irin taimakon gwamna da goyon bayansa suna matukar kara wa sojoji kwarin guiwa a fagen fama
  • Gwamna Zulum ya taya GOC murnan samun ƙarin girma tare da sauran sojojin da lamarin ya shafa kwanan nan

Borno - Kwamandan runduna ta 7 na hukumar sojojin Najeriya, Manjo Janar, A.A. Eyitayo, ya bayyana cewa ba tare da roko ba, Zulum ya tallafawa sojoji a lokuta da dama.

GOC na runduna ta 7 yace gwamnan Borno, Farfesa Zulum, ya taimaka wa sojoji da kayayyaki da sauran taimako, domin ƙara musu kwarin guiwa a yaƙi da Boko Haram.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sabon rahoto ya fallasa yadda Hafsoshin soji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai

Daily Trust ta rahoto cewa kwamandan ya yi wannan furucin ne yayin da gwamnan ya kai ziyara hedkwatar sojojin dake Maiduguri ranar Lahadi.

Gwamna Zulum
Yadda Gwamna Zulum ya tallafawa sojoji ba tare da sun roke shi ba, Shugaban dakarun soji Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa Zulum ya halarci taro na musamman da sojojin suka shirya domin taya GOC murnar ƙarin girman da ya samu zuwa Manjo Janar.

Kwamandan sojojin yace:

"A lokuta da dama ba tare da mun zo nema ba, ka kawo mana ɗauki da taimakon kayayyaki."
"Ta hanyar cikakken goyon baya da taimakon ka (Zulum), sojoji na ƙara samun kwarin guiwa wajen ƙara kaimi a fagen yaki."

Daga nan kuma, GOC din ya roki Zulum ya isar da sakon yabo da jinjinar sojoji ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da hafsan sojin ƙasa, bisa zakulo sojojin da suka cancanta da ƙara musu girma.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Zulum ya taya sojojin murna

Gwamna Zulum, ya taya muƙaddashin GOC murna, da kuma sauran jami'an sojin da suka samu ƙarin girma a baya-bayan nan, yace mutanen Borno sun yi farin ciki da haka.

A cewar Zulum, jami'an tsaro na rundunar soji da sauran hukumomin tsaro sun cancanci a taimaka musu da kuma ƙara musu karfin guiwa.

Gwamnan ya kuma dora nasarar gwamnatinsa da namijin kokarin sojoji wajen dawo da zaman lafiya, wanda a cewarsa, hakan ne yasa aka samu nasarar sake farfaɗo da yankuna 18 a faɗin Borno.

A wani labarin na daban kuma Sabon bincike ya bankaɗo yadda shugabannin sojoji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai

Wani sabon rahoto da CDD ta fitar, ya bayyana yadda shugabannin soji da ake naɗawa suka yi sama da makudan kudi cikin shekara 20.

Rahoton ya nuna cewa ta hanyar kwangilar siyo makamai a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun yi sama da dala biliyan $15bn.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Asali: Legit.ng

Online view pixel