Bayan kimanin kwanaki 120, Dogo Giɗe ya sako ɗaliban Yauri 28 da malamansu biyu da ke hannunsa

Bayan kimanin kwanaki 120, Dogo Giɗe ya sako ɗaliban Yauri 28 da malamansu biyu da ke hannunsa

  • Daga karshe an sako daliban makarantar sakandare ta Yauri da malamansu biyu
  • Yan bindige masu yi wa Dogo Gide biyayya ne suka sace daliban kimanin watanni hudu
  • An dade ana ta kokarin tattaunawa da sulhu domin ganin an sako su amma sai yanzu

Kebbi - Kasurgumin dan bindiga, Dogo Gide, ya sako daliban makarantar sakandare na tarayya da ke Birnin Yauri, a ranar Laraba bayan sun shafe kwanaki a hannunsa, Daily Trust ta ruwaito

An sace su ne kimanin watanni hudu a makarantarsu a lokacin da yan bindigan suka ci galaba kan jami'an tsaro a makarantarsu da ke wani kauye a jihar Kebbi.

Bayan kimanin watanni huɗu, an sako ɗaliban Yauri 28 da malamansu biyu
An sako ɗaliban Yauri 28 da malamansu biyu. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Read also

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Daily Trust ta ruwaito cewa an saki wasu daga cikin daliban a makon da ta gabata, bayan tattaunawa da wasu daga cikin iyayen yaran da suka ce an yi musu alkawarin sada su da yayansu.

Amma daga bisani ba a sako su ba domin an gaza cimma matsaya tsakanin masu tattaunawa da shugaban yan bindigan.

Majiyoyi sun ce za a kai su Birnin Kebbi a ranar Alhamis

Jaridar ta ruwaito cewa a ranar Lahadi, an sako dalibai biyu da malamansu biyu - mace da namiji - daga dajin inda jami'an tsaro da likitoci suka tarbe su a Kotonkoro, wani gari da ke kusa da dajin da yan bindigan suka yi kaka-gida.

Wadanda aka sako na baya-bayan sun isa Kotonkoro misalin karfe 8.30 na daren ranar Laraba, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.

Majiyar ta ce:

"Daga Kotonkoro, za a kai su Kontagora, kafin gobe (yau da safe) a tafi da su Birnin Kebbi."

Read also

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun harbe sarakuna biyu har lahira a wurin taro

Amma wata majiyar daban ta ce akwai yiwuwar daliban da malaman da aka sako Minna za a kai su, babban birnin jihar Neja, sai Abuja kafin daga bisani a kai su Birnin Kebbi.

Daily Trust ta ruwaito cewa fiye da mutum 32 ne Gide ya sace. An sako shida daga cikinsu da farko a yayin da ake tattaunawa da yan bindigan.

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Read also

Dalla-dalla: Yadda 'yan bindiga suka yi wa jama'a kisan kiyashi a kasuwar Sokoto

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Source: Legit

Online view pixel