Yadda magidanci ya kashe matarsa da duka bayan sun samu saɓani a Nasarawa

Yadda magidanci ya kashe matarsa da duka bayan sun samu saɓani a Nasarawa

  • Wani magidanci a unguwar Sabon Pegi-Shubu, a karamar hukumar Lafia ta Arewa, Jihar Nasarawa ya halaka matansa
  • Ovye Yakubu ya kama matarsa ne da duka bayan ya dawo gida ya tarar ta kira kafinta ya gyara mata ragar da ke taga don hana sauro shiga daki
  • Tuni dama dai Yakubu ya dade yana rikici da matarsa kan gidansu da suke zaune har ta kai sun kai batun kotu don a raba musu gardama

Nasarawa - Mutanen unguwar Sabon Pegi-Shubu, a karamar hukumar Lafia ta Arewa, Jihar Nasarawa, a ranar Juma'a sun shiga jimami da alhini bayan wani magidanci ya yi matarsa mai 'ya'ya uku duka har ta mutu bayan sabani ya shiga tsakaninsu, rahoton Vanguard.

An gano cewa rikicin ya samo asali ne a lokacin da matar auren, marigayiya Esther Aya ta kira wani kafinta domin ya gyara tagar gidan saboda sauro su dena shiga, da mijin ya dawo sai ya umurci kafintan ya dena aikin, hakan ya fusata matar.

Yadda magidanci ya kashe matarsa da duka bayan sun samu sabani a Nasarawa
Wani mutum ya kashe matarsa da duka a Nasarawa bayan sakamakon sabani da ya shiga tsakaninsu. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Kafintan ya magantu kan abin da ya gani

Vanguard ta rahoto cewa wani da ya yi magana amma ya nemi a boye sunansa, kuma ya yi ikirarin shine kafintan ya ce mijin marigayiya Esther ya fatattake shi yayin da ya ke kokarin gyara ragar da ke tagar gidan.

Mrs Esther Aya, malaman makarantar sakandare, Doka, wani gari da ke karamar hukumar Lafia ta Arewa, ta fara rikici da mijinta kan wanene ya mallaki gidansu da ke Sabo Pegi hakan yasa sun tafi kotu.

Marigayiyar, kafin rasuwar ta, a cewar makwabtanta ta rame kuma da ganinta tana cikin damuwa saboda irin tashin hankalin da ta ke fuskanta a hannun mijinta.

Yan sanda sun tabbatar da afkuwar lamarin

Rundunar yan sanda ta Jihar Nasarawa ta tabbatar da kama Ovye Yakubu, kan zarginsa da kashe matarsa Esther Aya a unguwar Sabon Pegi-Shabu a Lafia.

Kakakin yan sandan Jihar, ASP Rahman Nansel wanda ya bada tabbatarwar cikin hira da aka yi da shi a ranar Asabar a Lafia, ya ce an kama wanda ake zargin a ranar Asabar bayan sun samu rahoton abin da ya faru.

Nansel ya kara da cewa ana gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya faru, yayin da gawar matar yana asibiti don a yi gwaje-gwaje.

Magidanci Ya Kashe 'Matarsa' Da Duka Saboda Cajan Waya a Abuja

A wani labari mai kama da wannan, wani mutum mai suna Hasan Taiwo, ya yi wa masoyiyarsa da suka zaune tare, Chibuzor Aloh, mai yara hudu, duka har sai da ta mutu saboda ta yi amfani da cajar wayansa ba tare da izininsa ba.

The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a unguwar Lugbe da ke birnin tarayya Abuja. Tuni dai labarin mutuwar matar ya bazu a garin a ranar Lahadi.

An bayyana cewa marigayiyar ta dauki cajan wayar masoyinta ne ba tare da izininsa ba, haka kuma ya fusata shi ya hau ta da duka ya mata mugun rauni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel