Magidanci Ya Kashe 'Matarsa' Da Duka Saboda Cajan Waya a Abuja

Magidanci Ya Kashe 'Matarsa' Da Duka Saboda Cajan Waya a Abuja

  • Wani mutum a birnin tarayya Abuja ya halaka mahaifiyar yaransa da duka saboda cajar waya
  • Mutumin mai suna Hasan Taiwo ya yi wa matar, Chibuzor Aloh, duka ne don ta dauki cajarsa ba da izininsa ba
  • Dukan ya yi mata ya saka ta suma, makwabta suka farfado da ita amma daga bisani ta ce ga garin ku bayan an kai ta asibiti

Lugbe, Abuja - Wani mutum mai suna Hasan Taiwo, ya yi wa masoyiyarsa da suka zaune tare, Chibuzor Aloh, mai yara hudu, duka har sai da ta mutu saboda ta yi amfani da cajar wayansa ba tare da izininsa ba.

The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a unguwar Lugbe da ke birnin tarayya Abuja. Tuni dai labarin mutuwar matar ya bazu a garin a ranar Lahadi.

Magidanci Ya Kashe 'Matarsa' Da Duka Saboda Cajan Waya a Abuja
Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

An bayyana cewa marigayiyar ta dauki cajan wayar masoyinta ne ba tare da izininsa ba, haka kuma ya fusata shi ya hau ta da duka ya mata mugun rauni.

Kara karanta wannan

Hatta Musa Ya Yi Hijira Saboda Fir'auna, Babu Laifi Don Igboho Ya Tsere, Afenifere

Dukan ya saka Aloh ta suma amma makwabta suka farfado da ita bayan yaranta sun fita waje sun sanar da mutane halin da ta ke ciki kamar yadda rahoton na The Punch ya zayyana.

Mutanen unguwa sun tabbatar da lamarin

Wani mazaunin unguwar da ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo ya ce:

"A ranar Laraba da ta gabata, mai gida ya yi wa matarsa duka saboda ta dauki cajar wayansa. Ya mata duka har sai da ta suma. Ya fita daga gidan ya bar ta a hakan. Yaransu suka sanar da makwabta wadanda suka bata taimakon farko ta farka.
"Daga baya an ji cewa bata tafi asibiti ba domin a duba ta bayan ta farfado, sannan ta rufe kanta a daki.
"Babu wanda ya san abin da ya faru. Amma a ranar Asabar, babban cikin yaranta ya kira makwabta suka garzaya da ita asibiti.

Kara karanta wannan

Mai 'Car Wash' ya ragargaza Benz GLC da aka kawo masa wanki bayan ya ari motar zuwa siyan abinci

"A cewar abin da aka fada mana, a mace aka kai ta asibitin. Sun ce mijin ya tsere. Gawar matan na dakin ajiye gawa na asibitin kasa."

Kakakin yan sandan Abuja, ASP Mariam Yusuf, ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Ta ce, "rundunar na bincike a halin yanzu."

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

A wani labarin mai kama da wannan, Jami'an yan sanda na jihar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.

Usman Hammawa, mazaunin yankin Jada a karamar hukumar Ganye ta jihar Adamawa, ya halaka matarsa ne ta hanyar buga kanta da bango, hakan yasa ta fadi sumammiya.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel