Sabon harin Zamfara: Mutane 36 aka kashe a yankin Bukkuyum – Gwamna Matawalle

Sabon harin Zamfara: Mutane 36 aka kashe a yankin Bukkuyum – Gwamna Matawalle

  • Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya ce mutane 36 'yan bindiga suka kashe a sabon harin da suka kai karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar
  • Matawalle ya kuma bayyana cewa suna da sunaye da bayanan mutanen da suka rasa rayukansu a harin
  • Ya kuma bayar da tabbacin ganin an mayar da dukkanin wadanda suka yi hijira daga wadannan kauyuka zuwa garuruwansu nan da mako daya

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana cewa mutane 36 'yan bindiga suka kashe a sabon harin da suka kai karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar.

A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, Matawalle ya bayyana cewa ya kai ziyarar gani da ido kananan hukumomin Anka da Bukkuyum domin tabbatar da irin ta'asar da maharan suka yi.

Kara karanta wannan

Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar

Sabon harin Zamfara: Mutane 36 aka kashe a yankin Bukkuyum – Gwamna Matawalle
Sabon harin Zamfara: Mutane 36 aka kashe a yankin Bukkuyum – Gwamna Matawalle Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Matawalle ya kuma bayyana cewa yanzu haka suna da sunaye da bayanai na mutanen da suka rasa rayukansu a harin.

Rahoton ya kuma kawo cewa gwamnan ya ce daga yankin Bukkuyum zai wuce Anka domin tabbatar da rahotannin da ke yawo na cewar an kashe sama da mutane 200.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karshe, ya bayar da tabbacin cewa zai yi iya kokarinsa domin ganin cewa an mayar da dukkanin wadanda suka yi hijira daga wadannan kauyuka zuwa garuruwansu nan da mako daya.

Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar

A halin da ake ciki, mun kawo cewa Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce za a tura manyan jiragen yaki da aka siyo daga Amurka zuwa jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga manyan hare-hare da aka kai fadin kauyuka 10 a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke Zamfara.

Kara karanta wannan

Kungiya ga Ortom: Ka mayar da hankali wurin biyan albashi a Benue, maimakon matsawa Buhari

Bayan duba sabbin sojin da aka dauka a fadin kananan hukumomi 14 a jihar a ranar Asabar, Matawalle ya yaba ma gwamnatin tarayya na ayyana yan bindiga a matsayin yan ta’adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel