Musulmi da Musulmi: Hadimin Tinubu ya magantu kan rade-radin da ake yi game da abokin takarar jagoran na APC

Musulmi da Musulmi: Hadimin Tinubu ya magantu kan rade-radin da ake yi game da abokin takarar jagoran na APC

  • Tunde Rahman, hadimin Bola Tinubu ya yi tsokaci a kan rahotannin cewa babban jagoran na APC zai zabi abokin takara Musulmi idan ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar
  • Rahman ya ce ya yi wuri da za a fara magana a kan wanda zai zamo abokin takarar ubangidan nasa duba ga cewar bai bayyana kudirinsa na yin takara ba a hukumance
  • Ana dai ganin Tinubu wanda ya kasance Musulmi zai zabi dan arewa Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben 2023

A yayin da ake tsaka da rade-radin cewa jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, zai zabi abokin takara Musulmi idan ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, hadiminsa, Tunde Rahman ya ce ya yi wuri da za a fara wannan hasashen.

Rahman ya bayyana hakan a cikin wani sako a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Ba matsala bane musulmi da musulmi su gaji Buhari da Osinbajo, inji kungiyar magoya bayan Tinubu

Musulmi da Musulmi: Hadimin Tinubu ya magantu kan rade-radin da ake yi game da abokin takarar jagoran na APC
Musulmi da Musulmi: Hadimin Tinubu ya magantu kan rade-radin da ake yi game da abokin takarar jagoran na APC Hoto: BBC.com

Ya fadi hakan ne yayin da aka nemi ya yi martani kan rahotannin cewa Tinubu, wanda ya kasance Musulmi zai dauki Musulmi dan arewa a matsayin abokin takara.

A baya mun ji cewa Darakta Janar na kungiyar magoya bayan Tinubu, Abdulmumin Jibrin, ya ce ba matsala bane idan Tinubu ya dauki Musulmi a matsayin abokin takararsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jibrin ya kara da cewar yan Najeriya za su zabi cancanta sama da kabila ko addini.

Sai dai a hira da jaridar Punch, kakakin Tinubu ya ce ya yi wuri da za a fara tattauna batun abokin takara alhalin tsohon gwamnan na Lagas bai fito fili ya kaddamar da aniyarsa na takara ba.

Ya ce:

“Mai girma, Asiwaju Bola Tinubu, bai riga ya ayyana aniyarsa na takarar shugaban kasa ba a hukumance, kamar yadda ya fadi a yan makkoni da suka gabata a Abuja, yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki daban-daban.

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu a tsaida Musulmi da Musulmi takara ba, sama da kasa za su hade inji CAN

“Ina ganin bai kamata mu yanke hukunci ba. Idan ya ayyana haka, sauran abubuwa za su biyo baya. Har sai ya aikata hakan zan bayar da shawarar cewa kada muyi ta rade-radi kan abokin takararsa.”

Ba za ta yiwu a tsaida Musulmi da Musulmi takara ba, sama da kasa za su hade - CAN

A gefe guda, kungiyar CAN ta kiristocin Najeriya ta yi gargadi cewa ba za ta amince a bar musulmai biyu su tsaya a tikitin takarar shugaban kasa a 2023 ba.

CAN tace idan har musulmi da musulmi suka tsaya a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa a zaben 2023, kasar nan za ta iya rugujewa.

Jaridar Punch ta rahoto kungiyar ta CAN ta na wannan bayani ne a matsayin martani ga Abdulmumin Jibrin wanda yake da irin wannan ra’ayin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel