Ba za ta yiwu a tsaida Musulmi da Musulmi takara ba, sama da kasa za su hade - CAN

Ba za ta yiwu a tsaida Musulmi da Musulmi takara ba, sama da kasa za su hade - CAN

  • Shugaban Kungiyar CAN na kiristocin Najeriya yace ba za su goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi ba
  • Mai magana da yawun bakin shugaban CAN, ya na ganin ba za ta yiwu addinin ‘yan takara ya zama daya ba
  • A ra’ayin Rabaren Bayo Oladeji, rikici zai barke idan aka nemi ayi hakan, kuma ba za a iya cin ma nasara ba

Abuja - Kungiyar CAN ta kiristocin Najeriya ta yi gargadi cewa ba za ta amince a bar musulmai biyu su tsaya a tikitin takarar shugaban kasa a 2023 ba.

CAN tace idan har musulmi da musulmi suka tsaya a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa a zaben 2023, kasar nan za ta iya rugujewa.

Jaridar Punch ta rahoto kungiyar ta CAN ta na wannan bayani ne a matsayin martani ga Abdulmumin Jibrin wanda yake da irin wannan ra’ayin.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

Hon. Jibrin wanda shi ne Darekta-Janar na kungiyar Tinubu Support Group ya na ganin Bola Tinubu zai iya tsayawa takara tare da musulmin mataimaki.

Kakakin shugaban CAN na kasa, Rabaren Bayo Oladeji yace yin hakan zai jefa Najeriya cikin tashin hankali, kuma ba za su goyi bayan wannan aiki ba.

Musulmi da Musulmi
Shugaba Buhari a Umrah Hoto: Femi Adesuna
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yanzu ba 1993 ba ne - CAN

Mai magana da yawun bakin shugaban kiristocin kasa yace ba zai yiwu a maimaita abin da MKO Abiola da Babagana Kingibe suka yi a shekarar 1993, yau ba.

Punch ta rahoto Oladeji yace ko a zaben 93' da aka yi hakan, a karshe SDP ba ta kare lafiya ba.

“’Yan siyasa za su iya su yi siyasarsu, amma mun fadi ra’ayinmu. Duk jam’iyyar da ta tsaida musulmi da musulmi ko kirista da kirista, za ta sha kasa.”

Kara karanta wannan

Hukuncin fadan ‘Happy Xmas’ ga kiristoci a musulunci daga bakin Dr. Sani Rijiyar-Lemu

“Yanzu ba 1993 ba ne, ko a lokacin da ake da tikitin musulmi da kirista, coci su na shan wahala. Allah kadai ya san iyaka adadin kiristocin da aka hallaka.
Tsarin mulki na son a samu daidaiton addinai. Idan su na son su yi tikitin musulmi da musulmi, su je su jarraba, za mu nuna masu kiristoci ‘yan gata ne.”

- Bayo Oladeji

Mulki na Allah ne - NSCIA

Amma a gefe guda, Punch ta rahoto cewa kungiyar NSCIA da ke karkashin jagorancin Sarkin Musulmi tace mulki na Allah SWT ne, kuma kowa na iya samu.

Darektan gudanarwa na NSCIA, Zubairu Ugwu ya bayyana cewa za su cigaba da kira a zauna lafiya, kuma su tabbatar nagari ne suka samu mulki a Najeriya.

Aiki ya na jiran Ayu a PDP

Yayin da aka fara shirye-shiryen zaben 2023, kun ji cewa jam’iyyar PDP za ta so tayi waje da APC. Amma akwai wasu abubuwan da ake bukatar Iyorchia Ayu ya yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

Sai shugabannin PDP sun yi da gaske kafin su iya sake karbe ragamar shugabanci. Dole a hana kusoshin jam'iyya canza sheka, kuma a lashe zabukan Ekiti da Osun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel