Da duminsa: Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60

Da duminsa: Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun sake kai hari kan mazauna a wasu kananan hukumomin jihar Zamfara
  • Rahoto ya nuna cewa kimann mutane sittin ake zargin sun rasa rayukansu yayinda wasu suka jikkata

Zamfara - Akalla mutum 60 ake zargin an kashe yayinda yan bindiga suka kai hari wasu kauyukan jihar Zamfara.

Daily Trust ta ruwaito cewa kauyukan da aka kai hari sun hada da Kurfa Danya, Kurfa Magaji Rafin Gero, Tungar Isa da Barayar Zaki a karamar hukumar Bukkuyum da karamar hukumar Anka.

Wani mazaunin Zamfara mai suna Babangida yace:

"Sun yiwo tururuwa kan babura suna harbin yan gari suna kona gidaje da runbunan abinci. Mazaunan musamman mata da yara sun gudu da kafafuwansu."
"Har yanzu bamu san inda gomman mutane suke ba. Kawo safiyar Alhamis, mutane na taruwa a Nassarawa Burkullu. Wasu sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga."

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

Da duminsa: Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60
Da duminsa: Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60
Asali: Facebook

Mazaunan sun kara da cewa sun fara tsintan gawawwakin wadanda aka kashe don musu jana'iza.

Sun ce mutane na tsoron shiga cikin daji kwaso wasu gawawwakin.

Suka ce:

"Wani Shugaban yan bindiga Shehu Bayade ne ya jagoranci harin, garkuwa da mutane da satar Shanu a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gumi na jihar."
"Mun yi imanin (Bello) Turji da yaransa ne suka gayyaci Shehu Bayade dajin. Sabida a tunaninsu mayar da dajin mabuyarsa zai hana jiragen Sojoji ganinsu sabanin inda suka gudu."

Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su

Wannan hari ya biyo bayan sakin mutum 52 da dan ta'adda Bello Turji yayi.

Bello Turji, gagararren dan bindigan jihar Zamfara, a ranar Litinin ya sako mutane 52 wadanda suka dade a hannunsa

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

"Wadanda aka sako din a halin yanzu ana fito da su daga daji zuwa wani wuri da aka yi yarjejeniya inda daga nan za a kai su garin Shinkafi.

"Motoci sun yi layi kuma an umarce su da su fara tafiya hanyar Maberiya, wani yanki da ke da nisan kilomita 5 daga gabashin garin Shinkafi," wani mazaunin yankin da ya bukaci a boye sunansa ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel