Sabon salo: Ministan Buhari ya fitar imel dinsa, ya roki 'yan Najeriya su fadi ra'ayinsu akan aikinsa

Sabon salo: Ministan Buhari ya fitar imel dinsa, ya roki 'yan Najeriya su fadi ra'ayinsu akan aikinsa

  • Ministan sufurin Najeriya ya fitar da adireshinsa na imel ga 'yan Najeriya domin su tura masa kokensu
  • Ya bayyana cewa, zai ji dadi idan 'yan Najeriya suka tura abin da suke ji game ayyukan ma'aikatarsa
  • Rahoton da muka samo ya bayyana adireshin tare da yadda ministan ya bayyana manufar daukar matakin

Abuja - Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a ranar Talata, ya saki adireshinsa na Imel ga al’ummar Najeriya, inda ya bukace su da su ba fadu ra’ayinsu kan ayyukan ma’aikatar da ke karkashinsa.

A cewar rahoton Vanguard, a wata sanarwa da ya fitar, Amaechi ya rubuta:

“Ina matukar godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, bisa damar da ya ba ni na yi wa kasa hidima a matsayin ministan sufuri.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Buhari ya kasa cika alkawurransa saboda bashi da mukarrabai nagari, Bashir Tofa

Ministan sufuri, Amaechi ya nemi a fadi aibinsa
Sabon salo: Ministan Buhari ya fitar imel dinsa, ya roki 'yan Najeriya su fadi ra'ayinsu akan aikinsa | Hoto: vanguardngr.com
“Babban abin da muka mayar da hankali a kai a matsayinmu na ma’aikata shi ne sake gyara layukan dogo da na ruwa da suka lalace wadanda su ne manyan hanyoyin sufuri da kuma hanyoyin samun kudaden shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Duk da haka, mun fahimci bukatar tantancewa da kuma sha’awar sani daga ’yan kasa yadda muka yi, kasancewar muna da hakki daga gareku.
“Saboda haka, ra’ayoyinku game da ayyukan da Ma’aikatar ta gudanar ya zuwa yanzu yana da muhimmanci a gare mu. Muna sha'awar sanin inda kuke jin mun yi nasara ko muna cin nasara, inda ya kamata mu inganta, ko kuma inda kuke jin mun gaza ko kuma muna gazawa.
“Hakkinmu ne da sha’awarmu ne mu ci gaba da ingantawa. Da fatan za a yi tura min imel a chibuikeamaechi128@gmail.com. Zan yi matukar godiya da wannan karimcin.”

Kara karanta wannan

Komai ya na iya faruwa a 2023 – Kwankwaso ya tanka masu rade-radin sake shiga APC

Kudi $36bn nike bukata in dinke Najeriya da layin dogo

Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa $36bn kadai yake bukata ya dinke Najeriya gaba daya da layin dogo.

Amaechi ya bayyana hakan ne da safiyar Juma'a, 31 ga Disamba, a shirin 'Good Morning Nigeria' na tashar NTA.

A cewarsa, ginin layin dogo aiki ne mai lakume kudi sosai shi yasa kamfanoni masu zaman kansu ba zasu iya zuba kudi ba.

Ya ce dalilin da ya sa Gwamnatin Buhari ke karban basussuka don yin aikin shine an samu dukiyoyin da aka mika matsayin jingina.

A wani labarin, a yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da koke-koke kan lalacewar tituna, hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (NNPC) ta yi yunkuri wajen gyara wasu tituna 21 na tarayyar kasar a dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida.

Matakin na NNPC wanda aka kiyasta zai ci Naira biliyan 621.2 ya samu amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ranar Laraba 27 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

The Cable ta ruwaito cewa Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje ne ya bayyana haka bayan taron FEC da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel