Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

  • Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tsufa ya fara kama shi amma ya gode wa Allah
  • Shugaba Buhari ya furta hakan ne yayin amsa tambayoyi daga manema labarai yayin tattaunawa da aka yi da shi a ranar Alhamis
  • Buhari, wanda a yanzu shekarunsa 79 ya ce sa'o'insa suna can suna hutuwa shima yana fatan ya samu hutun bayan wa'adinsa don ya hidimtawa Najeriya daidai gwargwado

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana fatan ya kammala wa'adin mulkinsa lafiya domin 'tsufa ya fara kama shi', Daily Trust ta ruwaito.

Buhari, wanda ya cika shekaru 79 a ranar 17 ga watan Disamban 2021, ya bayyana hakan ne yayin amsa tambaya a tattaunawa da aka yi da shi a NTA, a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Buhari: PDP za ta kwace mulki daga hannun APC idan har bata magance rikice-rikicenta ba

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah
Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah, Buhari. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Game da shekaru na, ina ganin sa'o'i na, yanzu suna hutawa ne, kuma ina tabbatar maka nima ina fatan ganin bayan watanni 17 nan gaba da zan samu in ɗan huta,' in ji shi.

Ya cigaba da cewa:

"Tsufa ya fara kama ni, aiki na awa shida, bakwai ko takwas kullum a ofis ba abu bane mai sauki a yanzu; akwai batun taron majalisar koli, da takardu daga jihohi daban-daban kusan ko wane mako. Gaskiya aiki ne mai wahala, amma kaman yadda na faɗa, ni na nemi aikin don haka ba zan koka ba.
"Na yi gwamna, na yi minista, kuma ga shi ina wa'adi na na biyu a matsayin shugaban kasa. Don, haka na zaga a aikin, don haka mai kuma ya rage in yi wa kasar? Na yi iya kokari na."

Kara karanta wannan

Ina son yan Najeriya suce na yi iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari

Buhari ya yanke hukunci na ƙarshe kan batun samar da 'yan sandan jihohi

A wani labarin, kun ji cewa a karo na biyu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da samar da ‘yan sandan yankuna, The Nation ta ruwaito.

Ya yarda da cewa jihohi da dama ba za su iya daukar nauyinsu ba kuma yana tsoron a yi amfani da su ta wata hanyar da bata dace ba.

‘Yan Najeriya da dama sun nuna bukatar samar da ‘yan sandan ciki har da gwamnonin jihohi don kawo karshen rashin tsaro da ya yi wa kasar nan katutu.

Samar da ‘yan sandan jiha wata hanya ce ta sauya tsarin tsaro kuma tuni wasu yankuna su ka samar da tasu mafitar kamar Amotekun da Ebube Agu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel