Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun jikkata wasu da dama a Zariya

Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun jikkata wasu da dama a Zariya

  • Yayin da sojoji ke cigaba da samun nasara kan yan bindiga a jihar Zamfara, a jihar Kaduna ba haka abin yake ba
  • Wasu miyagun yan bindiga sun farmaki wani kauye a yankin Zariya, sun kashe mutum hudu tare da jikkata wasu da dama
  • Wani mazaunin kauyen ya tabbatar da cewa sun yi gaggawar kiran layin yan sanda, amma ba su zo ba sai bayan harin

Kaduna - Wasu dandanzon yan bindiga sun farmaki kauyen Kofar Kana, dake karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum hudu.

Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Nigerian cewa yan ta'addan sun kai hari kauyen da misalin karfe 10:00 na daren ranar Litinin, inda suka bude wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

Ku yiwa 'yayanku tarbiyya bisa al'adunmu, Lai Mohammed ya yi kira ga iyaye

Rahoto ya bayyana cewa bayan wutar da suka bude wa mutane, yan bindigan sun tattara dabbobi da dama sun yi cikin daji da su.

Jihar Kaduna
Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun jikkata wasu da dama a Zariya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Wani mazaunin yankin da ya zanta da manema labarai bisa sharaɗin boye bayanansa, yace sun kira layin taimakon gaggawa na yan sanda amma ba'a ɗaga ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun kira lambobin neman agajin gaggawa na hukumar yan sanda amma babu wanda ya ɗaga. Jami'an yan sanda sun iso ne lokacin da yan bindiga suka gama ta'addancin su."
"Aƙalla mutum 24 muka ɗauka zuwa babban Asibitin Gambo Sawaba dake Kofar Gayan. Mutum 4 daga ciki sun mutu sanadiyyar raunukan da suka samu a harin."
"Yan bindigan sun yi awon gaba da shanu da yawa na wasu Fulani, waɗan da suka zo yankin a baya-bayan nan."

Ko hukumar yan sanda ta samu rahoto?

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutum 7 yan gida daya, da wasu mutum 17 a sabon harin jihar Kaduna

Har zuwa yanzun da muka haɗa wannan rahoton, kakakin rundunar yan sanda reshen Kaduna, Muhammad Jalige, bai ɗaga kiran wayan da aka masa ba.

A wani labarin kuma daya daga cikin mutanen da suka kubuta daga hannun Bello Turji ya bayyana gaskiyar yadda suka kubuta

Mutumin mai suna Ibrahim Rowa yace yana tsaka da kokarin kwashe gyaɗa da ya noma a gonarsa wasu yan bindiga suka sace shi, kwanaki 23 kenan da suka shuɗe.

Mutane sama da 50 ne suka kubuta biyo bayan luguden wutan sojoji a sansanonin yan bindiga dake kusa da inda suke a dazukan Zamfara da Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel