Innalillahi wa inna ilaihi raji'un: Fitaccen Shehin Tijjaniyya a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un: Fitaccen Shehin Tijjaniyya a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

  • Wani fitaccen malamin darikar Tijjaniya a jihar Kwara, Sheikh AbdulSalam, ya riga mu gidan gaskiya ranar Laraba
  • Daruruwan dubbannin mutane sun halarci Jana'izar Shehin Malamin, wanda ke da mabiya sosai kuma mutane ke matukar girmama shi
  • Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya jajanta wa al'ummar musulmai, tare da fatan samun rahama ga marigayin

Kwara - Shahararren malamin addinin musulunci a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Sheikh Shuaib AbdulSalam, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sheikh AbdulSalam ya rasu ne jiya Laraba, 5 ga watan Janairu, 2022, da safe bayan fama da jinya yana da shekaru 68 a duniya.

Sheikh AbdulSalam
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un: Fitaccen Shehin Tijjaniyya a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya Hoto: Abdulazeez Yinka Oniyangi
Asali: Facebook

Marigayi Malam AbdulSalam, Sufi ne kuma limamin Maraba, ya kasance babban Shehin Tijjaniya, wanda ke da magoya baya masu tarin yawa kuma mutane na matukar girmama shi a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Ba matsala bane musulmi da musulmi su gaji Buhari da Osinbajo, inji kungiyar magoya bayan Tinubu

Dandazon mutane sun halarci Janaza

Mabiya addinin musulunci da yawan gaske ne suka halarci Sallar Jana'izar marigayin, wacce ta tara manyan mutane daga gwamnati da kuma addini.

Jami'an tsaro sun jigata sosai wajen kula da dandazom mutane da cunkoson abun hawa a Oniyangi, hanyar gidan Sarki, inda aka gudanar da sallar jana'izar mamacin.

Jihar Kwara ta yi babban rashi

Sakataren kwamitin kungiyoyin musulmai (CMO), na jihar Kwara, Sheikh Yusuf Murtadoh, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tsoron Allah.

Kuma musulmi wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga harkokin ilimi da kuma gyara rayuwar al'ummar musulmai fiye da tunani,, a cewar shi.

Kazalika, gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana mutuwar malamin da babban abin takaici, tare da addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma sa Aljanna ta zame masa makoma.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yaba da aikin Buni, ya ba da shawara kan shirin zaben 2023 ga Buhari

A wani labarin kuma Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Kungiyar matan Arewa sun tabbatar wa gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi goyon bayan su a babban zaben 2023.

Matan karkashin kungiyar YBN sun bayyana cewa gwamna Bello ya nuna zai iya jagorancin Najeriya duba da nasarorinsa a Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel