Biloniya Dantata ya soki tsarin gwamnatin Najeriya, ya ce ta gaza

Biloniya Dantata ya soki tsarin gwamnatin Najeriya, ya ce ta gaza

  • Fitaccen biloniya, Alhaji Aminu Dantata, ya ce salon mulkin shugabancin kasa da ake yi a halin yanzu a Najeriya na gaza gaba daya
  • Dantata ya furta hakan ne da kungiyar dattawan arewa suka je yi masa ta’aziyyar Sani Dangote, Bashir Tofa da sauran manyan da suka rasu
  • A cewarsa, akwai bukatar dattawan arewa su hada kai wurin kawo hanyar kawo karshen matsalolin da Najeriya ke fuskanta

Kano - Biloniyan dan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata, ya ce salon mulkin da ake tafiyar da Najeriya ya gaza, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Dantata ya furta hakan ne yayin da ya karba bakuncin kungiyar dattawan arewa wadanda su ka je ta’aziyyar Sani Dangote, Othman Bashir Tofa da sauran manyan mutanen jihar Kano da su ka mutu babu dadewa.

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Biloniya Dantata ya soki tsarin gwamnatin Najeriya, ya ce ta gaza
Biloniya Dantata ya soki tsarin gwamnatin Najeriya, ya ce ta gaza. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce akwai bukatar dattawan arewa su hada kai tare da sauran ‘yan Najeriya wurin kawo wata mafita da za ta kawo karshen matsalolin Najeriya.

“Za ku yarda idan nace yanayin salon da ake bi wurin mulkin Najeriya ya gaza don haka ya kamata su sauya wani salon na daban,” a cewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda suka je ta’aziyyar sun hada da Janar Sale Maina, Hakeem Baba Ahmed, shugaban kungiyar hadin kan arewa, Nastura Shariff, Dr Sadiq Gombe, Hajiya Najaatu Mohammed da sauransu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar dattawan arewan ta kai ziyara ga sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, mataimakin gwamna Nasiru Gawuna da Alhaji Yahya Hamma.

Buhari: Abinda na sanar da Gwamnan Oyo yayin da ya ziyarce ni kan rikicin manoma da makiyaya

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda suka yi da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, wurin kawo tsarikan gargajiya domin shawo kan matsalar makiyaya da manoma, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Ministan Buhari ya fitar imel dinsa, ya roki 'yan Najeriya su fadi ra'ayinsu akan aikinsa

Buhari ya ce gwamnoni biyu sun ziyarci Aso Rock kan rikicin, amma ya shawarce su da su yi kokarin komawa su shawo kan matsalar ta hanyar shugabannin gargajiya da kuma makiyayan da suke hana zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Shugaban kasan bai fadi sunan dayan gwamnan ba, amma Daily Trust ta tuna cewa jihohin Ondo da Ogun ne suke fuskantar matsalar makiyaya da manoma wanda hakan ya kawo asarar rayuka da kadarori.

Asali: Legit.ng

Online view pixel