Buhari: Abinda na sanar da Gwamnan Oyo yayin da ya ziyarce ni kan rikicin manoma da makiyaya

Buhari: Abinda na sanar da Gwamnan Oyo yayin da ya ziyarce ni kan rikicin manoma da makiyaya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya kai masa korafi kan rikicin manoma da makiyaya a jiharsa
  • Buhari ya sanar da cewa, ya umarci Makinde da su koma yankunansu su shawo kan matsalar a gargajiyance tare da bankado tushen al'amarin
  • A cewar Buhari, tuni ya san manoma da makiyaya suna da matukar jituwa da fahimtar juna, amma kwatsam yanzu babu ita

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda suka yi da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, wurin kawo tsarikan gargajiya domin shawo kan matsalar makiyaya da manoma, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Buhari ya ce gwamnoni biyu sun ziyarci Aso Rock kan rikicin, amma ya shawarce su da su yi kokarin komawa su shawo kan matsalar ta hanyar shugabannin gargajiya da kuma makiyayan da suke hana zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Kara karanta wannan

2023: Osinbajo ne ya dace ya gaji Buhari, Dan majalisar Kano, Hafizu Kawu

Buhari: Abinda na sanar da Gwamnan Oyo yayin da ya ziyarce ni kan rikicin manoma da makiyaya
Buhari: Abinda na sanar da Gwamnan Oyo yayin da ya ziyarce ni kan rikicin manoma da makiyaya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban kasan bai fadi sunan dayan gwamnan ba, amma Daily Trust ta tuna cewa jihohin Ondo da Ogun ne suke fuskantar matsalar makiyaya da manoma wanda hakan ya kawo asarar rayuka da kadarori.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Dapo Abiodun ya ziyarci Buhari a watan Fabrairu da ta gabata kan rikicin makiyaya da manoma a Yewaland.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a watan Janairun 2021, Makinde ya ziyarci Buhari bayan rikicin karamar hukumar Ibarapa da ke Oyo.

A yayin rikicin kabilancin na Ibarapaland, mai rajin kare hakkin Yarabawa, Sunday Igboho, ya tsinkayi gidan Sarkin Fulani da ke Igangan, Saliu Abdul-Kadri, inda yace Yarabawa ba za su cigaba da jure kashe-kashe a kasar su ba.

Daga bisani, an kori AbdulKadir daga gidansa inda wasu mabiyan Igboho suka banka wa yankin wuta.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

Igboho ya tsinkayi jihohin Ogun, Osun da Ondo inda suka bai wa Fulani notis kan su bar yankin kudu maso yamma.

Wannan rikicin ya tada hankula, lamarin da yasa aka fara nuna bukatar kafa 'yan sandan jiha.

Ana tsaka da wannan lamarin, Makinde ya ziyarci Buhari domin neman taimakon ganin bayan wannan rikicin.

A wata tattaunawa ta musamman da Channels TV, Buhari ya ce manoma da makiyaya suna da alaka mai kyau tare da fahimtar juna, lamarin da yasa ya ke mamakin abinda ya lalata alakar.

Ya ce, ya sanar da Makinde da dayan gwamnan da su je tare da nemo abinda ya lalata alakar nan wurin shugabannin yankunan.

Shugaban kasar ya ce sarakunan gargajiya dole ne su taka rawar gani wurin tabbatar da zaman lafiya a yankunan.

Ya kara da kira garesu da su rungumi tattaunawa a matsayin hanyar shawo kan rikicin makiyaya da manoma a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Babban faston Najeriya ya bayyana wanda zai gaji Buhari

Tuna baya: Buhari ya kasa cika alkawurransa saboda bashi da mukarrabai nagari, Bashir Tofa

A wani labari na daban, Alhaji Bashir Othman Tofa wanda ya tsaya takarar shugaban kasa karkashin NRC a zaben da aka yi ranar 12 ga watan Yunin 1993 wanda aka rushe sakamakon zaben ya tattauna da Daily Trust a watan Maris din 2020.

Sun yi maganganu akan rashin tsaron da Najeriya take fama da su da kuma batun rashin cika alkawuran da shugaba Buhari ya yi.

Kamar yadda Tofa yace:

“Zan maimaita abinda na dade ina fadi. Shugaban kasa ya rasa mataimakan da suka dace su tallafa masa ya tabbatar da alkawuran da ya dauka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel