Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai

  • Wasu yan bindiga sun kashe mutum 13 a jihar Benuwai, cikin harda jariri ɗan wata uku kacal
  • Shugaban ƙaramar hukumar Guma, wanda lamarin ya faru a yankinsa, ya tabbatar da kai harin
  • Wani shaida ya bayyyana cewa wasu yan bindiga sun buɗe wuta a kan wata mota dake gabansu

Yan bindiga sun harbe jariri ɗan wata uku kacal har lahira tare da wasu mutum 12 a hari daban-daban a wasu ƙauyukan karamar hukumar Guma, jihar Benuwai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Barka da Sallah: Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Yan Bautar Kasa NYSC da Kyautar Kudi da Shanu a Daura

Yan bindigan sun buɗe wuta kan matafiya a hanyar Uikpam–Umenger da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Talata, inda suka kashe mutum biyar, cikinsu harda jariri, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Hakanan, sauran mutum 8 ɗin an kashe su ne a yankin Branch Ude da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Talata (Jiya).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jiha a Gidanta

Yan bindiga sun kashe mutum 13 a Benuwai
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shugaban ƙaramar hukumar Guma, Caleb Aba, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho, cewa:

"Eh dagaske ne an kai hari jiya Talata. Mutane sun je jana'aiza a Torkula yayin da suke kan hanyar komawa gida ne wasu yan bindiga suka buɗe musu wuta, mutum 5 suka mutu."

"Hakazalika da misalim ƙarfe 10 na daren jiya, an sake kai wani hari a Branch Ude, inda aka kashe mutum 8, wanda hakan yasa mutanen da aka kashe suka kai 13 a jiya kaɗai."

"Akwai wasu mutum biyu da suka ji rauni a rahoton da na samu, kuma yanzun haka an kai su asibiti domin kulawa da lafiyarsu."

Shaidu sun tabbatar da harin

Wani shaida, David Mzer, yace suna kan hanya a mota shi da wasu abokansa yayin da suka fahinci an buɗe wa motar gabansu wuta, inda hakan ya tilasta musu juya wa.

Mzer ya ƙara da cewa direban motar ya samu nasarar kaucewa harsashin kuma ya ƙara gudu domin tseratar da rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Kwararren Likita a Jihar Kogi

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Jirgin Yakin Sojojin Sama NAF da Ya Fado a Zamfara

Yace: "Yan bindigan sun toshe hanyar, sannan suka buɗe wuta kan wata motar Toyota Picnic, inda suka kashe jariri ɗan wata uku sannan suka harbi mahaifiyarsa a guiwa."

"Na kusa da ni, wanda daga shi sai Toyota Picnic ɗin, yana ganin haka ya yi gaggawar juyawa ya koma Uipkam."

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda na jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, ta bayyana cewa har yanzun basu sami rahoto dangane da lamarin ba.

A wani labarin kuma Masarauta a Jihar Kano Ta Dakatad Da Wani Basarake Saboda Zargi

Masarautar Karaye dake jihar Kano ta dakatad da magajin garin ƙauyen Butu-Butu saboda wani zargi.

Hakimin Rimin Gado, Alhaji Tukur, shine ya kai korafin basaraken kan zargin haddasa fitina tsakanin mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: