An ci gaba da shagalin biki bayan an sako amaryar da aka sace a Filato

An ci gaba da shagalin biki bayan an sako amaryar da aka sace a Filato

  • Mai shirin zama amarya wacce wasu da ba a san ko su waye ba suka yi awon gaba da ita ta samu yanci
  • Tuni aka ci gaba da shagalin bikin nata bayan bayyanarta a daren ranar Litinin
  • Kakakin 'yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Gabriel Ogiba, ya tabbatar da dawowar amaryar amma ya ce suna gudanar da bincike don gano gaskiyar lamari

Filato - Rahotanni sun kawo cewa an sako wata amarya, Farmat Paul, wacce aka sace a ranar Lahadi a gidan fasto dinta da ke garin Ngyong da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato.

An yi garkuwa da ita ne a gidan faston inda ake sanya ran za ta kwana a ranar jajiberin aurenta, Daily Trust ta ruwaito.

An ci gaba da shagalin biki bayan an sako amaryar da aka sace a Filato
An ci gaba da shagalin biki bayan an sako amaryar da aka sace a Filato Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta kuma rahoto cewa an saki amaryar ne a daren ranar Litinin inda aka ci gaba da shagalin bikin jim kadan bayan sakin nata.

Kara karanta wannan

Cin zarafi: Yadda kafar intanet a Indiya ta tallata yin gwanjon matan muslumai a kasar

Da aka tuntube shi kan batun sakin amaryar, Kakakin yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel Ogiba, ya ce wacce abun ya cika da ita ta dawo gida amma bai yi bayanin ko an biya kudin fansa kafin sakin nata ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Litinin, ASP Gabriel ya ce kodai dai babu wani korafi da aka shigar ofishin yan sanda kan lamarin a hukumance, sun ji labari sannan suka shiga aiki don binciken al’amarin batan nata.

Ya ce:

“Ba lallai ne ya kasance lamari na garkuwa da mutane ba saboda akwai lokacin da mace ta je kwana a gidan wani namiji Sannan kowa na ta fadin cewa an yi garkuwa da ita ne. Muna binciken inda ta shiga amma ba Za mu yi gaggawan cewa an yi garkuwa da ita bane. Mun shiga aiki."

Wata majiya, wacce ta kuma tabbatar da sakin nata, ta ce an biya kudin fansa amma bata iya tabbatar da ko nawa aka biya ba.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria

Tirkashi: An sace Amarya awanni kafin daura aure a jihar Filato

A baya mun kawo cewa wata budurwa dake shirin zama Amarya, Farmat Paul, ta shiga hannun masu garkuwa da mutane awanni kaɗan kafin ɗaura aurenta a jihar Filato.

Daily Trust tace an sace Amaryan, wacce ke zaune a yankin ƙaramar hukumar Bokkos, jihar Filato, a gidan Fasto, inda ake tsammanin zata kwana kafin a ɗaura mata aure.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana wa manema labarai cewa yan bindigan sun farmaki gidan Faston da misalin ƙarfe 10:45 na dare, kuma suka yi awon gaba da Amaryan kaɗai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel