Yanzu: An harbe 2, an sace 'yan China 3 a yayin da 'yan bindiga suka kai hari wurin aikin lankarki na Zungeru

Yanzu: An harbe 2, an sace 'yan China 3 a yayin da 'yan bindiga suka kai hari wurin aikin lankarki na Zungeru

  • Wasu hatsabiban yan bindiga sun kai wa ma'aikata hari a wurin da ake aikin wutan lantarki na Zungeru a karamar hukumar Wushishi a jihar Niger
  • Maharan sun bindige mutane biyu, sannan sun yi awon gaba da wasu ma'aikata 'yan kasar China 3 bayan musayar wuta da jami'an tsaro
  • Kakakin yan sandan jihar Niger, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da afkuwar harin ya kuma ce an tura jami'an tsaro su bi sahun maharan su ceto wadanda aka sace

Niger - A kalla mutane biyu ne aka bindige yayin da aka sace yan kasar China uku da ke aikin samar da wutan lankarki a dam din Sino da ke Zungeru a karamar hukumar Wushishi ta jihar Niger.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu da ake zargin yan bindiga ne suka kai wa ma'aikatan hari yayin da suke aiki kan wata wayar sadar da lantarki a kauyen Gussase a yammacin ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

Yanzu: An harbe 2, an sace 'yan China 3 a yayin da 'yan bindiga suka kai hari wurin aikin lankarki na Zungeru
Yan bindiga sun kai hari wurin aikin lankarki a Zungeru, sun bindige mutum 2, sun yi awon gaba da 3. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Sakataren gwamnatin jihar Niger, Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da kai harin amma bai iya tabbatar da cewa ko an rasa rayuka ba.

Yan sanda sun tabbatar da harin

Kakakin yan sandan jihar Niger, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da afkuwar harin yana mai cewa an harbi dan China da dan Najeriya daya, kuma an nemi wasu yan China ba a gansu ba bayan musayar wuta tsakanin yan sanda da yan bindigan.

Abiodun ya kara da cewa:

"A yayin da ake kokarin tseratar da mutane lokacin musayar wutar, an nemi wasu 'yan kasar China uku ba a gansu ba a halin yanzu."

Kakakin yan sandan ya ce gamayyar yan sanda da sojoji na musamman da ke Zungeru tuni sun bazama domin farautar yan bindigan da nufin ceto wadanda yan bindigan suka sace.

Kara karanta wannan

An ci gaba da shagalin biki bayan an sako amaryar da aka sace a Filato

An kaddamar da aikin samar da wutan lantarkin ne na Megawatt 700 kan kudi Dalla Biliyan 1.3, a matakai guda hudu.

Kamfanonin CNEEC da SINOHYDRO ke aikin gina dam din samar da lantarkin na Megawatt 700 a jihar Niger a Najeriya.

Aikin idan an kammala zai zama dam din samar da lantarki na biyu bayan na Kainji dam da ke samar da wuta Megawatt 760.

Yana daya daga cikin manyan ayyukan lantarki a Afirka daga bankin Exim na China.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel