Daga karshe: 'Yan kasa sun tafka zanga-zanga, firaministan Sudan yayi murabus

Daga karshe: 'Yan kasa sun tafka zanga-zanga, firaministan Sudan yayi murabus

  • Ana ci gaba da fargabar cewa Sudan na gab da fuskantar bala'i yayin da bangarorin gwamnatin rikon kwaryar kasar ke fuskantar tashe-tashen hankula
  • Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa firaministan kasar da ke nahiyar Afirka ya yi murabus daga ofishinsa a ranar Lahadi 2 ga watan Janairu
  • Firaministan, wato Abdalla Hamdok ya koka da cewa kokarin ceto Sudan daga barazana ba ya haifar da sakamakon da ake so ko kuma da mai ido

Sudan - Firaminista Abdalla Hamdok na Sudan a ranar Lahadi 2 ga watan Janairu ya yi murabus daga ofishinsa a daidai lokacin da al'ummar kasar ke cikin tashin hankali watanni bayan juyin mulki.

Da yake jawabi ga 'yan kasar a ranar Lahadi, Hamdok ya yi ikirarin cewa ya yi iya kokarinsa don hana kasar zamewa zuwa firgici, in ji rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Ba dani ba: Lauyan Sunday Igboho ya zare hannunsa a rikicinsu da gwamnatin Buhari

Abdalla Hamdok
'Yan kasa sun tafka zanga-zanga, firaministan Sudan yayi murabus | Hoto:channelstv
Asali: UGC

A cewar jaridar Guardian, ya bayyana fargabar cewa kasar "tana haye wani yanayi mai hadari wanda ke barazana ga rayuwarta baki daya."

Hamdok da aka bayyana a matsayin fuskar farar hular Sudan ya yi misali da "durkushewar dakaru na siyasa da rigingimu tsakanin bangarorin mika mulki."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hamdok ya ci gaba da cewa "duk da duk abin da aka yi don cimma matsaya... hakan bai faru ba".

Sojoji sun tsare Firayim ministan Sudan da wasu jiga-jigan gwamnatinsa

A wani labarin, rahotanni masu girgiza zukatan da ke zuwa a halin yanzu shi ne na daurin talalan da sojojin kasar Sudan suka yi wa Firayin Ministan Abdallah Hamdok.

Kamar yadda Al-Jazeera ta wallafa, sojojin sun yi ram da Hamdok tare da wasu daga cikin ministocinsa a sa'o'in farko na ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon dan takarar gwamna a jihar Arewa

Daga cikin jami'an gwamnatin Sudan da sojoji suka kama, akwai ministan masana'antu, Ibrahim Al-Sheikh, ministan yada labarai, Hamza Baloul da kuma mai bai wa Hamdok shawara kan yada labarai, Faisal Mohammed Saleh.

Asali: Legit.ng

Online view pixel