Tirkashi: 'Yan sanda sun kwace bindigogin harbo jiragen sama 109 daga 'yan bindigan Katsina

Tirkashi: 'Yan sanda sun kwace bindigogin harbo jiragen sama 109 daga 'yan bindigan Katsina

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta ce ta kwato bindigogin harbo jiragen sama guda 109 da sauran miyagun makamai daga ‘yan bindiga
  • A cewar kakakin rundunar, SP Gambo Isa, yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin a Katsina, lamarin ya auku ne tsakanin watan Janairu zuwa Disamba
  • Yace an kama wadanda ake zargin masu laifi ne guda 999 a jihar, wanda cikinsu an gurfanar da mutane 874 a kotu ana kokarin yanke musu hukuncin da ya dace

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kwace fiye da bindigogin harbo jirgi 109 daga hannun ‘yan bindiga tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2021 cikin jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isa, ya bayyana hakan yayin tattaunawa da wakilin NAN a ranar Litinin a Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayani: Mazauna unguwa a Legas sun yi zanga-zanga saboda girke musu 'yan sanda

Tirkashi: 'Yan sanda sun kwace bindgogin harbo jiragen sama 109 a Katsina
Tirkashi: 'Yan sanda sun kwace bindgogin harbo jiragen sama 109 a Katsina. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A cewarsa, an kama mutane 999 a fadin jihar yayin da aka amshe bindigogin harbo jirgi 109 da GPMG guda 4 duk a wannan datsin, The Guardian ta ruwaito.

“Sannan an kwace bindigogi kirar AK-47 guda 44, LAR guda daya, bindigogin toka guda 20, da kuma 689 rounds na 7.62mm ammunition wanda AK-47 take amfani, dabbobi 1,243 ciki har da shanu 867, tumaki 352, awakai 24 da jaki guda daya daga hannun ‘yan bindigan.
“Yanzu haka an kama mutane 999 da ake zargin su na da hannu a aikata laifuka 608, an gurfanar 874 daga cikinsu gaban kotu a cikin jihar.
“Sannan kuma akwai mutane 157 da aka kama bisa zarginsu da zama ‘yan fashi, an gurfanar da mutane 145 gaban kotu yayin da ake bincike a kan sauran 12.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

“An yi ram da mutane 65 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, 63 daga cikinsu su na gaban kotu sai kuma 2 da ake ci gaba da bincike akan su.
“Mun samu nasarar kama barayin shanu 244 wadanda yanzu haka an gurfanar da 230 daga cikinsu gaban kotu yayin da ake bincike akan sauran mutane 14 daga cikinsu,” a cewarsa.

Vanguard ta ruwaito cewa, Isa ya kula da cewa yayin sintiri, sun kama ‘yan bindiga 38 bayan sun yi musayar wuta da ‘yan sanda, sai dai jami’an rundunar ‘yan sandan guda 5 sun rasa rayukansu.

A cewarsa, sun kama masu laifi 246, cikinsu ana zargin mutum 195 da fyade da sauran laifuka, 63 daga cikinsu kuma safarar mutane ake zarginsu da aikatawa sannan an tura su ofishin NAPTIP da ke jihar Kano.

Kakakin ya kara da bayyana yadda rundunar ta ceto mutane 215 wadanda aka yi garkuwa da su sai kuma ta amshe ababen hawa 20 da ake zargin sace su aka yi, 18 da ake zargin na ‘yan bindiga ne.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara

Asali: Legit.ng

Online view pixel