Bayani: Mazauna unguwa a Legas sun yi zanga-zanga saboda girke musu 'yan sanda

Bayani: Mazauna unguwa a Legas sun yi zanga-zanga saboda girke musu 'yan sanda

  • A wani yankin jihar Legas, wasu mazauna sun nuna kin jinin ajiye 'yan sanda a unguwarsu na tsawon lokaci
  • Sun koka kan yadda basu san dalilin ajiye wadannan 'yan sanda ba, lamarin da ya tayar da hankulan jama'a
  • An gansu suna zanga-zanga dauke da allunan nuna kin jinin haka, tare da daukar matakai a kofofin shiga yankin

Legas - Mazauna rukunin gidaje na Magodo Phase II da ke Legas sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da kasancewar ‘yan sanda sama da 50 dauke da makamai a yankinsu.

Hukumar gudanarwar yankin a safiyar Talata ta rufe kofofi biyu da ke shiga cikin jerangiyar gidajen, The Nation ta ruwaito.

Ana zanga-zanga a Legas saboda 'yan sanda
Da Duminsa: Mazauna unguwa a Legas sun yi zanga-zanga saboda kawo musu 'yan sanda | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Rufewar ya haifar da katsewa da cunkoson ababen hawa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutum 7 yan gida daya, da wasu mutum 17 a sabon harin jihar Kaduna

An bar mutane su fita daga cikin jerangiyar gidajen, amma an hana su shiga ciki.

Mazauna yankin sun dauki allunan nuna rashin jin dadinsu da yadda aka dasa 'yan sanda a yankin.

Sun nemi sanin dalilin aje ‘yan sandan da aka ce suna cikin jerangiyar gidajen tun watan jiya.

Wasu daga cikin rubuce-rubucen sun kasance kamar haka:

“Babban Lauyan Jihar Legas na tuhumar wadanda ke da hannu wajen mamaye Magodo Phase 2 da ka yi alkawari ba bisa ka’ida ba.”
“Magodo Phase 2 ya kasance a karkashin rundunar ‘yan sandan kwantar da tarzoma ta IGP na tsawon makonni uku.”

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban kungiyar mazauna Magodo, Bajo Osinubi, ya ce:

“Mun kira mutanenmu domin yin zanga-zanga a safiyar yau.
“Sama da ‘yan sanda 50 ne ke zaune a jerangiyar gidajen. Muna son ’yan sandan su fice daga unguwarmu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

“Babu wani lamari na yin garkuwa da mutane, tarzoma, amma me yasa har yanzu suke nan? Muna son su fita daga cikin unguwarmu."
“Muna so mu zauna lafiya. Wannan abu ne tsakanin gwamnatin jihar Legas da dangin Adeyiga.
“Muna karkashin kamu; ‘Yan sandan sun shafe makonni biyu suna nan, sun zo ne a watan Disamba domin su karbi kadarori a madadin iyalan Adeyiga da sauran su.
"Tun daga lokacin, mun tuntubi manyan mutane don shiga tsakani kuma mu fitar da 'yan sanda daga gidajenmu.
“Mune wadanda abin ya shafa, har ma a cikin gidajenmu. 'Yan sanda sun kasance a nan. Ba sa sararawa."

Sai dai a rahoton jaridar Punch gwamnatin jihar Legas ta bayyana mamayar a matsayin wanda bai dace ba, ta kuma sha alwashin gurfanar da wadanda ke da hannu a cikinsa.

An gurfanar da wata mata a kotu kan 'cin zarafin' sufetan 'yan sanda a Legas

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun shiga har gida sun sace matar ɗan uwan kwamishina da ɗansa

A wani labarin, ‘yan sanda sun gurfanar da wata mata gaban Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas bayan cin zarafin sifetan ‘yan sanda, Punch ta ruwaito.

Wacce ake karar ta na fuskantar laifuka biyu ne, daya na cin zarafi sai kuma tayar da zaune tsaye.

Mai gabatar da kara, ASP Clement Okuiomose ya sanar da kotu cewa wacce ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Disamba da misalin karfe 10 na safe a haraban kotun majistaren da ke Badagry a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel