Jami'ar Najeriya ta bawa tubabbun karuwai 5,000 da marasa galihu guraben karatu kyauta

Jami'ar Najeriya ta bawa tubabbun karuwai 5,000 da marasa galihu guraben karatu kyauta

  • Jami’ar Tansian da ke Umunya a jihar Anambra tare da hadin gwiwar Chartered Institute of Educational Practitioners da ke Ingila, CIEPUK, ta dauki nauyin karatun tubabbun karuwai 5,000 da sauran marasa galihu
  • Farfesa Marcel Ezenwoye, shugaban CIEPUK na kasa, ya sanar da hakan a ranar Talata a Abuja yayin tattaunawa da manema labarai, inda yace za a tattaro mutane 5,000 dinne daga jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya, Abuja
  • Gwamnatin ko wacce jiha ce zata tura sunaye sannan za a kwashe watanni uku ana horar da su sana’o’i iri-iri na hannu tare da basu duk wasu abubuwan da zasu bukata daga ranar 25 ga watan Fabrairu

Anambra - Jami’ar Tansian da ke Umunya a jihar Anambra tare da hadin gwiwar Chartered Insititute of Education Practitioners da ke Ingila, CIEPUK za ta dauki nauyin karatun tubabbun karuwai 5,000 da sauran marasa galihu.

Kara karanta wannan

Ba za ku tsira ba: Buhari ya magantu kan masu koma wa APC don gujewa EFCC

Farfesa Marcel Ezenwoye, shugaban CIEPUK na kasa ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Talata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Jami'ar Najeriya ta bawa tubabbun karuwai 5,000 da marasa galihu guraben karatu kyauta
Jami’ar Anambra ta dauki nauyin karatun tubabbun karuwai 5,000 da marasa galihu. Hoto: The Nation

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Ezenwoye ya ce an tattaro sunayen wadanda za su amfana da tallafin ne daga jihohi 36 da ke kasar tare da babban birnin tarayya, Abuja.

A cewarsa:

“Gwamnatin ko wacce jiha ta tura sunayen wadanda za su amfana kuma zasu kwashe watanni uku ne da farko ana horar da su tare da koya musu sana’o’in hannu wadanda za a tanadi duk abubuwan da zasu bukata.
“Za a kasa su kashi-kashi ne inda za su dinga zuwa taron horarwa a cikin cibiyoyi biyu da ke arewa da kudancin Najeriya na kasar nan, za a fara ne da kashi na farko daga ranar 26 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani mummunan hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 19 a jihar Kano

“Watanni ukun da za a yi ana koyar da sana’o’in hannun, za a koyar da hada takalma, hada sabulu, hada man shafawa, rubuce-rubuce, gyaran bidiyo, koyar noma da kiwo da sauransu.”

Ya ce har girke-girke da shirin fim za a koya musu

A cewarsa sauran abubuwan da za a koya sun hada da iya shirin fim, harkar kafinta, gyaran wuta, rini, wanki da guga, hada kayan gyara girki, aski da harkar girke-girken sha’ani.

Shugaban CIEPUK ya ce za a iya horar da mutane 185,000 a kashi na farkon daliban da za a dauka.

A cewarsa, CIEPUK zata dauki nauyin kudin makaranta, kudin dakunan kwana, kudin kulawa da lafiyarsu da tsaron duk wani dalibi. Sai kuma gwamnatin jihohinsu su dauki nauyin kudin ci da shan su na tsawon watanni ukun da za a horar dasu.

Hakan zai taimaka wurin rage rashin ayyukan yi a kasa baki daya

Ya kara da cewa ana sa ran bayan samun horarwar za su iya samar wa yankunansu Naira biliyan 200 a ko wacce shekara baya ga kudaden da ayyukansu za su samar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

Ezenwoye ya ce hakan zai tallafa wa rayuwarsu kuma ya hanasu aikata duk wasu miyagun laifuka sannan zai taimaka wurin gyaran tarbiyyar yara mata da marasa galihu a kasar nan.

Ya ce jami’ar tare da taimakon CIEPUK za ta kawo ci gaba ga yankunan kasar nan daga ko wacce kabila, yanki ko kuma jinsi. Don haka kasa zata bunkasa ta wannan hanyar.

Ya ce ya yi imani da cewa Ubangiji zai ci gaba da taimakon kowa kuma ya samar wa marasa hali mafita a kasar nan.

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

A wani labarin, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wasu masu tone kabari su sace sassan jikin mamata sun shiga hannu

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel