IPOB ta haramta cin naman shanun Fulani yayin bukukuwa a kudu maso gabashin Najeriya

IPOB ta haramta cin naman shanun Fulani yayin bukukuwa a kudu maso gabashin Najeriya

  • Kungiyar 'yan aware masu son kafa kasar Biafra, Indigenous People of Biafra, IPOB, ta haramta amfani da naman shanu daga arewa
  • Kungiyar ta sanar da hakan ne ta bakin mai magana da yawunta, Emma Powerful tana mai cewa daga yanzu shanun da ake kiwo a kudu za a rika amfani da shi
  • Kungiyar ta gargadi mutanen yankin kan karya dokar tana mai cewa duk wanda aka samu da yana saba dokar zai dandana kudarsa

Haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, ta haramta cin naman shanun Fulani a yankin kudu maso gabashin Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

IPOB, cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin ta bakin mai magana da yawunta, Emma Powerful, ya ce dokar haramci zai fara aiki a watan Afrilu.

IPOB ta haramta cin naman shanun Fulani a kudu maso gabashin Najeriya
Kungiyar IPOB ta hana cin naman shanu daga arewa a Kudancin Najeriya. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Kannywood: Hafsat Shehu ta bayyana halin da ta shiga bayan rasuwar mijinta, Marigayi Ahmad S. Nuhu

A cewar kungiyar, shanun kawai da ake kiwo a yankin ne za a rika amfani da su wuraren biki ko sha'ani a yankin.

"Daga wannan watan, ba za mu rika amfani da shanun Fulani ba domin yin wani biki ko sha'ani a kasar Biafra.
"Za mu rika amfani da shanun mu da ake kiwo a nan domin bukukuwan.
"Ya zama dole masu sarautun mu na gargajiya, malaman addini da kungiyoyi na garuruwa su tabbatar wannan sakon ya isa ga dukkan mutane," a cewar wani sashi na sanarwan.

Duk wanda aka kama yana saba dokar zai yaba wa aya zakinta, IPOB

Kungiyar ta kuma gargadi mambobinta, wanda ta ce wasu daga cikinsu na son karya dokoki ko rashin biyayya ga umurnin shugabanni, NewsWireNGR ta ruwaito.

A cewar IPOB, 'daga yanzu an dena daga kafa kuma ba za a rangwanta wa duk wanda aka samu yana laifi ba.'

Mai magana da yawun na IPOB ya yi addu'ar Allah ya tsare, kiyayye kuma ya yi wa shugabansu Nnamdi Kanu jagora a gwagwarmayarsa na samo musu 'yanci.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

'Yan bindiga sun kai wa fasinjoji hari a jirgin ruwa, sun yi musu fashi sun kuma sace jirgin

A wani labarin, 'yan bindiga sun afka wa wani jirgin kasa mai dauke da fasinjoji a ranar jejiberin sabuwar shekara a Bayelsa, Daily Trust ta ruwaito.

Jirgin mai dauke da fasinjoji 14 ya bar Yenagoa yana hanyarsa na zuwa karamar hukumar Twon Brass a yayin da yan bindigan suka kai musu hari, kamar yadda kamfanin dillancin Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Sun tsere da injin mai karfin horsepower 115 kirar Yamaha da ke jirgin ruwan sannan suka kwace wa fasinjojin dukkan abubuwa masu muhimmanci da suke dauke da su, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel