Kannywood: Hafsat Shehu ta bayyana halin da ta shiga bayan rasuwar mijinta, Marigayi Ahmad S. Nuhu

Kannywood: Hafsat Shehu ta bayyana halin da ta shiga bayan rasuwar mijinta, Marigayi Ahmad S. Nuhu

  • Hafsat Shehu, tsohuwar matar fitaccen tauraron Kannywood, Ahmad S. Nuhu, ta bayyana mawuyacin halin da ta shiga bayan rasuwarsa
  • Tsohuwar jarumar fim din ta ce ta fada cikin matukar bakin ciki ta yadda idan ta ga wasu mutane suna dariya takan tambayi mahaifiya cewa yaushe itama za ta soma dariya
  • Tauraron ya rasu ne ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007 sakamakon hatsarin mota a garin Azare na jihar Bauchi

Tsohuwar jaruma kuma matar fitaccen jarumin Kannywood, Ahmad S. Nuhu, ta bayyana mawuyacin halin da ta shiga bayan rasuwarsa.

Hafsat ta bayyana cewa labarin mutuwar marigayin wani abu ne mai ciwo da zafi da bata so ayi mata zancensa ma ko kuma a tambayeta game da shi.

A hira da tayi da sashin Hausa na BBC, jarumar ta ce ko shakkka babu Ahmad ya nuna mata so da kauna tare da mutunta a 'yan zamanda suka yi na shekara daya da rabi.

Kara karanta wannan

Ina son sanya tufafin matata, cewar wani magidanci da ya caba ado da kayan matarsa

Kannywood: Hafsat Shehu ta bayyana halin da ta shiga bayan rasuwar mijinta, Marigayi Ahmad S. Nuhu
Kannywood: Hafsat Shehu ta bayyana halin da ta shiga bayan rasuwar mijinta, Marigayi Ahmad S. Nuhu Hoto: Hausaloaded.com
Asali: UGC

Hafsat ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Labarin mutuwar Ahmed wani abu ne mai tsananin ciwo da zafi da radadi da bana hirar, bana son wani yayi mun, bana son wani ya tambaye ni. Ko wakar Ahmed aka sa sai in kalli mutum inga mai nayi mai, sai dai kawai na tuna shi nayi mai addu’a.
"Wani labari ne mai dimautar da mutum da ga karancin shekaru toh dai Alhamdulillah, astagafirulla, subhanallah ba dai abun da zan ce sai dai na ce Allah ya ji kan Ahmad, amma a kullun idan na zauna, na dai yi rashin masoyi.
"Farko dai Ahmad ya tafi Maiduguri, da ya zo Azare ya kirani yace toh fah Hafsat ga mu a Azare, sai na tambaye shi Ina ne Azare, sai ya ce mun wani kauye ne gaba da Wudil, sai ya ce mun Hafsat kin Ina son ki, nace mai eh Ahmad na son kana sona wannan wani irin magana ne, shikenan maganarmu ta karshe dani da shi.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

"Sai naji Ina jin zafi Ina jin sanyi, Ina jin yunwa, naje na dafa indomie guda daya na kawo falo, nasa da tukunyan a cikin bargo Ina ci na barta.
"Sai wani Danjuma ya zo sai yace mun ina wayata take, nace mai ga wayata, sai nace mai menene, yace dauko wayarki mu tafi gidan Ali, nace mai Ahmad ya rasu.
"So shine abun da ya faru, ba wani ne ya gaya mun ba don akwai abun da a jikinka na Za ka ji.
"Toh na shiga wani irin yanayi lokacin Ina takaba, akwai wata Asmau ita take kwanciya a bayana idan na zo na kwanta a bakin katifa, sai inji kamar ana kwashe ni, idan naga mutum yana dariya sai in tambayi mamanmu ni yaushe zan fara yin dariya, sai tace za ki yi lokaci ne.
"Ina tuna Ahmad koda mutum ne ya tsayar dani Ina tafiya yace Ina sonki sai na tuna Ahmad, saboda Ahmad mutum ne da yake daraja mace, yake mutunta mace, yake ba mace duk wani girmanta, yake dai so ya ga rayuwar mace a cikin inganci. Babu abun da zan yi wa Ahmad sai dai addu’a."

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

Jarumar ta kuma bayyana cewa a cikin shekara daya da watanni shida da suka yi tare da marigayin a matsayin mata da miji tayi bari sau biyu.

Haka kuma ta ce bayan rasuwarsa tayi aure sau biyu amma Allah bai nufi zaman nasu ba, amma ta ce mutuwar auren nata bashi da alaka da marigayin.

A yau 1 ga watan Janairun 2022 ne jarumin yake cika shekara 15 da rasuwa.

Matan aure na iya kai karar mazajensu kan kwanciya da su ta karfi-da yaji – Lauya

A wani labari na daban, wani lauya kuma tsohon sakataren labaran kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Benin, Douglas Ogbankwa, ya bayyana cewa duk mutumin da ya taba matarsa ba yadda ya kamata ba na iya fuskantar laifin lalata da matarsa.

Ogbankwa ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga 'yan jarida a ranar Alhamis kan ko yana iya yiwuwa mace ta zargi mujinta da laifin lalata a Najeriya, duba ga al'adarmu.

Kara karanta wannan

Bai zo a littafi mai tsarki ba: Kirista ta caccaki masu bikin Kirsimeti

Ya ce kafin a kafa dokar hana cin zarafin jama’a (VAPP) a wasu jihohin tarayya, baya bisa ka'idar doka a zargi miji da yin lalata da matarsa, rahoton 21stcenturychronicle.

Asali: Legit.ng

Online view pixel