Yan bindiga sun bindige Jigon APC har lahira jim kadan bayan ya kammala addu'o'i

Yan bindiga sun bindige Jigon APC har lahira jim kadan bayan ya kammala addu'o'i

  • Wasu miyagun yan bindiga sun tare jigon APC a jihar Akwa Ibom, sun harbe shi har lahira ranar Jumu'a
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, Odiko Macdon, yace ɗan mamacin ya kawo rahoton yadda lamarin ya faru
  • Kwamishinan yan sanda na jihar, Andrew Amiengheme, ya bada umarnin tsaurara bincike kan lamarin

Akwa Ibom - Jigon jam'iyyar APC, Mista Otu Inyang, ya rasa rayuwarsa bayan wasu yan bindiga sun bude masa wuta a kauyen Ikot Udoma, karamar hukumar Iket, jihar Akwa Ibom.

Dailytrust ta rahoto cewa maharan sun bindige shi ne jim kaɗan bayan ya kammala addu'o'in sabuwar shekara a coci.

Rahoto yace Yan bindigan sun bibiyi Jigon APC a jihar suka harbe shi mintuna kaɗan kafin shigar sabuwar shekara yayin da yake kan hanyar koma wa gida bayan halartan addu'o'i a cocin Qua Iboe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Yan bindiga
Yan bindiga sun bindige Jigon APC har lahira jim kadan bayan ya kammala addu'o'i Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Haka nan kuma rahoton ya bayyana cewa mamacin ne ya yi addu'ar rufe wa a cocin amma mitoci kaɗan kafin karisawarsa gida maharan suka tare shi, suka bude masa wuta.

Shugaban kungiyar mutanen Ekid kuma tsohon ɗan takarar gwamna, Dakta Samuel Udonsek, ya bayyana mamacin da jagoran al'umma nagari.

Punch ta rahoto shi yace:

"Wannan labarin ya jefa ni cikin rashin jin daɗi da takaici, zan iya cewa a yankin Ekid ba mu saba ganin irin wannan lamarin ba."
"Ina masa Addu'a Allah ya gafarta masa ya karbi kyawawan ayyukansa kuma ya sa shi a cikin gidan aljanna."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin yan sanda na jihar, SP Odiko Macdon, ya bayyana lamarin da abin takaici, kuma ya sha alwashin gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun shiga har gida sun sace matar ɗan uwan kwamishina da ɗansa

Macdon ya kara da cewa kwamishinan yan sanda, Andrew Amiengheme, ya umarci mataimakinsa ya gudanar da tsattsauran bincike kan lamarin.

Kakakin yan sandan yace:

"Eh dagaske ne, an harbe mutumin har lahira yayin da yake kan hanyar komawa gida bayan kammala addu'o'in ƙarshen shekara a cocinsa."
Ɗan sa ya kawo mana rahoto da safe cewa mahaifinsa da mahifiyarsa na kan hanyar dawowa gida wasu yan bindiga suka farmake su, suka harbe mahaifinsa a kai."
"Kwamishinan yan sanda, Andrew Amiengheme, ya umarci mataimakinsa ya gudanar da bincike kuma ya tabbar an gurfanar da masu hannu a kisan."

A wani labarin kuma Gwamnan PDP ya tsallake Atiku, ya bayyana wanda PDP zata baiwa takara daga Arewa a 2023

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace Allah ba zai gafarta wa PDP ba matukar jam'iyyar ta sake watsi da kiran yan Najeriya game da wanda suke so.

Wike yace yan Najeriya daga kowane sashi na kira ga PDP ta tsayar da gwamna Bala Muhammed na Bauchi a 2023.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sun yi awon gaba da matan aure da yan mata a sabon harin jihar Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel