Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun sace akalla mutum 18 a Kaduna

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun sace akalla mutum 18 a Kaduna

  • Duk da nasarar da jami'an tsaro ke kara samu kan yan ta'adda a sassan Najeriya, har yanzun ta'addancin yan bindiga kara ta'azzara yake
  • Rahoto daga jihar Kaduna ya nuna cewa wasu yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, kuma sun sace akalla 18 a kauyen Udawa dake Chikun
  • Wani shugaban yankin ya bayyana cewa maharan sun haɗa matan aure, yan mata da samari sun tafi da su yayin harin

Kaduna - Yan bindiga sun kashe mutum daya, kuma sun sace wasu 18 cikin su har da matan aure a kauyen Angwar Zalla Udawa, karamar hukumar Chikun a jigar Kaduna.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan sun kai hari kauyen wanda ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 12:30 na daren ranar Lahadi.

Wani shugaban al'umma a kauyen na Udawa, Muhammad Umaru. wanda ya tabbatar da lamarin, ya bayyana sunan wanda aka kashe da, Bala Jaja.

Jihar Kaduna
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun sace akalla mutum 18 a Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Haka nan kuma ya kara da cewa matan aure, samari da yan mata na daga cikin waɗan da maharan suka yi awon gaba da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malam Umaru ya bayyana cewa har yanzun yan bindigan ba su nemi iyalan waɗan da suke sace ba awanni bayan harin.

Tribune Online ta rahoto Umaru yace:

"Yanzun nan na dawo daga ƙauyen, kuma har yanzun maharan ba su tuntuɓi iyalan kowa ba daga cikin waɗan da suka sace."

Shin gwamnati na da masaniya?

Har yanzun babu wani bayani a hukumance daga gwamnatin jihar Kaduna da kuma hukumar yan sanda game da harin.

Kazalika kakakin rundunar yan sandan reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai ɗaya jerin kiran wayan da akai masa ba.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun hallaka Basarake da wasu mutane a sabon harin jihar Zamfara

Wasu miyagun yan bindiga sun kashe basarake a wani sabon hari da suka kai yankin masarautar Bungudu, jihar Zamfara.

Mazauna kauyen Gada sun bayyana cewa maharan sun cinna wuta a motocin masarauta da kuma kayan abincin da suka taras.

Asali: Legit.ng

Online view pixel