Yan sanda sun ceto daliban Islamiyya 21 daga hannun yan bindiga

Yan sanda sun ceto daliban Islamiyya 21 daga hannun yan bindiga

  • An ceto dalibai 21 cikin dimbin matafiyan da yan bindiga suka sace ranar Juma'a a hanyar Katsina
  • Hukumar yan sanda ya bayyana cewa har yanzu Malamin daliban na hannun yan bindigan tsare
  • Hukumar tace ta samu labarin yan bindigan sun tare motoci biyar kuma sun kwashe fasinjojin dake ciki

Zamfara - Jami'an yan sanda a jihar Zamfara sun samu nasarar ceto daliban Islamiyya 21 da aka sace a hanyar Gusau-Tsafe-Funtuwa ranar Juma'a.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya bayyana hakan a jawabin da ya sake ranar Asabar, rahoton TheCable.

Shehu yace an ceto daliban ne bayan musayar wuta da yan bindigan.

Daliban Islamiyya 21 da aka sace a kauyen Kuccheri
Yan sanda sun ceto daliban Islamiyya 21 da aka sace a kauyen Kuccheri daga hannun yan bindiga Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A cewarsa, daliban Islamiyyan da Malaminsu na hanyar tafiya daga Rini, Bakura zuwa Katsina lokacin da yan bindigan suka taresu a hanya kuma sukayi awon gaba da su.

Ya kara da cewa har yanzu Malamin Islamiyyan, direban motar da wasu fasinja na hannun yan bindigan har yanzu.

A jawabinsa yace:

"A ranar 31 ga Disamba, 2021, an samu kira daga garin Kucheri cewa yan binbidga sun tare titin Gusau-Funtua kuma sun sace matafiyan motoci biyar."
"Jami'an yan sanda tare da Sojoji suka garzaya wajen inda suka yi musayar wuta da yan bindigan."
"Yan sandan sun samu nasarar ceto yara 21 da wasu mata biyu wadanda suka taho daga garin Rini a karamar hukumar Bakura don zuwa Almajiranci Katsina, tare da Malaminsu Lawali Ibrahim."
"Malamin da Direban motar Hummer Bus na hannun yan bindigan har yanzu."

Yan sanda sun ceto daliban Islamiyya 21
Yan sanda sun ceto daliban Islamiyya 21 da aka sace a kauyen Kuccheri daga hannun yan bindiga
Asali: Facebook

Shehu yace Kwamishanan yan sandan jihar ya tura karin jami'a ceto sauran wadanda ke tsare tare da cafko yan bindigan

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Yan sanda sun bindige yan bindiga 38 har lahira a jihar Katsina

Bam ya tarwatsa kasurguman shugabannin 'yan bindigan Zamfara

A wani labarin, wani dan bindiga da ya yi kaurin suna a yankin Birnin Magaji da ke jihar Zamfara, Alhaji Auta, ya halaka a wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama.

An kuma hallaka da dama daga cikin ’yan tawagarsa a yayin farmakin da suka kai wa sansaninsa da ke Jama’are Bayan Dutchi, a gundumar Nasarawa Mailayi a Jihar Zamfara, a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel