Nasrun minallah: Yan sanda sun bindige yan bindiga 38 har lahira a jihar Katsina

Nasrun minallah: Yan sanda sun bindige yan bindiga 38 har lahira a jihar Katsina

  • Hukumar yan sandan jihar Katsina ta bayyana nasarorin da ta samu a 2021 da suka hada da hallaka yan bindiga akalla 38
  • Kwamishinan yan sanda na jihar, Sanusi Buba, yace jami'an yan sanda biyar sun rasa rayukansu a musayar wuta da dama
  • Yace yan sandan sun samu nasarar damke yan bindiga, masu garkuwa, da barayin shanu da dama, wasu na gaban kotu

Katsina - Aƙalla yan bindiga 38 suka mutu yayin da jami'an yan sanda biyar suka rasa rayukansu a hare-hare daban-daban a jihar Katsina.

Daily Trust tace kwamishinan yan sandan jihar, Sanusi Buba, shine ya bayyana haka a wani taron manema labarai na musamman da aka shirya.

A wurin taron wanda ya gudana ranar Alhamis, kwamishinan ya samu wakilcin kakakin rundunar yan sanda reshen Katsina, SP Gambo Isa.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Gwarazan yan sanda sun damke kasurgumin dan bindiga da ya addabi Zamfara

Jihar Katsina
Nasrun minallah: Yan sanda sun bindige yan bindiga 38 har lahira a jihar Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kwamishinan yace:

"Babu tantama wannan shi ne lokaci mafi kalubale ga hukumar yan sanda, duk da haka jami'ai sun samu nasarori a kan ayyukan yan bindiga, satar mutane, fashi da makami da sauran manyan laifuka a jihar."
"A shekarar 2021 mun samu raguwar aikata manyan laifuka idan aka kwatanta da shekarar baya."
"A wannan lokacin akalla yan ta'adda 38 jami'ai suka bindige har lahira, yayin da yan sanda biyar suka rasu a musayar wuta daban-daban."

Yan bindiga nawa yan sanda suka kama?

CP ya kara da cewa rundunar yan sanda ta kame waɗan da ake zargi 999 dake da alaƙa da kai hare-hare 608, yayin da 874 daga cikin su na gaban kotu suna jiran hukunci.

Yace hukumar ta kuma damke yan fashi da makami 157 kuma tuni ta gurfanar da 145 daga cikinsu yayin da jami'ai ke cigaba da bincike kan 12.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Buhari ya amince a ɗauki ƙarin 'yan sanda 10,000 aiki a Najeriya

"Mutanen da ake zargi da satar mutane domin neman kudin fansa 65 suka shiga hannu, kuma 63 daga ciki na gaban kotu, sauran biyu kuma ana cigaba da bincike a kansu."

Haka nan kuma, kwamishinan yace yan sanda sun cafke barayin shanu 244, 230 na gaban alkali, yayin da sauran 14 ke karkashin bincike.

Kwamishinan ya bayyana dumbin nasarorin da hukumar yan sanda ta jihar Katsina ta samu shekarar 2021.

A wani labarin na daban kuma Jami'an NSCDC sun gano gawarwakin matasa uku a Kogin jihar Benuwai

Rahotanni sun bayyana cewa a tun ranar kirsimeti matasan suka tattaru a bakin kogin domin gudanar da shagalin murna wanda gwamnatin jiha ta haramta.

Jami'an tsaro sun yi yunkurin hana su amma yawan su ya zarce na jami'an, daga baya aka nemi wasu daga cikin matasan aka rasa, inda daga baya aka gano gawar uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel