Matan aure na iya kai karar mazajensu kan kwanciya da su ta karfi-da yaji – Lauya

Matan aure na iya kai karar mazajensu kan kwanciya da su ta karfi-da yaji – Lauya

  • Wani lauya mai suna Douglas Ogbankwa, ya bayyana cewa matan aure na iya kai karar mazajensu kan kwanciya da su ta karfi-da yaji
  • Lauyan ya yi ikirarin cewa duk mutumin da ya taba matarsa ba yadda ya kamata ba na iya fuskantar laifin lalata da ita
  • Ya ce hakan ya samo asali ne bayan kafa dokar hana cin zarafin jama’a (VAPP)

Wani lauya kuma tsohon sakataren labaran kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Benin, Douglas Ogbankwa, ya bayyana cewa duk mutumin da ya taba matarsa ba yadda ya kamata ba na iya fuskantar laifin lalata da matarsa.

Ogbankwa ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga 'yan jarida a ranar Alhamis kan ko yana iya yiwuwa mace ta zargi mujinta da laifin lalata a Najeriya, duba ga al'adarmu.

Kara karanta wannan

Ina son sanya tufafin matata, cewar wani magidanci da ya caba ado da kayan matarsa

Ya ce kafin a kafa dokar hana cin zarafin jama’a (VAPP) a wasu jihohin tarayya, baya bisa ka'idar doka a zargi miji da yin lalata da matarsa, rahoton 21stcenturychronicle.

Matan aure na iya kai karar mazajensu kan kwanciya da su ta karfi-da yaji – Lauya
Matan aure na iya kai karar mazajensu kan kwanciya da su ta karfi-da yaji – Lauya Hoto: 21stcenturychronicle
Asali: UGC

Lauyan ya ce hakan ya samo asali ne saboda wasu kebabbun abubuwa da dokar hukunta masu laifi ta kafa a wasu sassan kasar, wanda ya hana a zargi miji da yi wa matarsa ​​fyade.

Sai dai kuma, ya ce bayan kafa dokar VAPP, lamarin ya sauya sosai kuma a yanzu ana iya kama miji da laifin yin lalata da matarsa koda kuma ta hanyar tabin da ake ganin baya bisa ka'ida ne.

Ya ce:

"Kafin zuwan dokar VAPP a wasu jihohi, ba za a iya kama miji da laifin lalata da matarsa ba.
“Hakan ya kasance ne saboda ware shi da dokar aikata laifuka ta yi a jihohin Kudu da kuma dokar Penal Code a jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

Kasa da sa'o'i 10 da aure, ango ya masgi amarya, ta tsere ta bar shi tare da kashe auren

“Doka ta tanadi cewa za a iya yin fyade ne kawai ga wacce take ba matar mutum ba.
"A yanzu dokar VAPP ta samar da kafar da ake kira lalata a tsakanin ma'aurata, wanda zai iya zama fyade ga miji ko mata. Yanzu an rarraba wannan a matsayin cin zarafin mutane."

Lauyan ya ce wannan ci gaban ya kuma haifar da raguwar shaidar da ake bukata don tabbatar da fyade.

Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa kan masu haike wa yara

A wani labarin, a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, gwamnatin jihar Jigawa ta amince da hukuncin kisan kai a kan masu lalata da kananan yara ta karfin tsiya.

Kwamishinan shari'a kuma Atoni Janar na jihar, Dr Musa Adamu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana cewa wadanda aka samu da laifin yin lalata da yara 'yan kasa da shekaru 10, za a yanke masu hukuncin kisan kai ba tare da mafita ba.

Kara karanta wannan

'Yan Arewa sun magantu, sun bayyana yadda suka fi kaunar mulkin Jonathan fiye da Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel