Kasa da sa'o'i 10 da aure, ango ya masgi amarya, ta tsere ta bar shi tare da kashe auren

Kasa da sa'o'i 10 da aure, ango ya masgi amarya, ta tsere ta bar shi tare da kashe auren

  • Aure tun yana dayensa ya kare bayan wani rikici ya hada angon da amaryar, lamarin da ya firgitar da mutane da dama
  • Mijin ya daki matarsa akan wani dalilin wanda suka ki bayyanawa a dakin Otal din da suka kama bayan bai wuci sa’o’i 10 ba da daurin auren
  • A bangaren matar, ta yi gaggawar daukar jakarta ta bar dakin tare da mijin kuma ta ce ta hakura da auren

Wasu sababbin aure sun rabu saboda wani rikici ya hada su bayan sa’o’i 10 da gama daurin aurensu.

Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ya wallafa labarin yadda lamarin ya auku saboda amaryar abokiyar aikinsa ce.

Kasa da sa'o'i 10 da aure, ango ya masgi amarya, ta tsere ta bar shi tare da kashe auren
Kasa da sa'o'i 10 da aure, ango ya masgi amarya, ta tsere ta bar shi tare da kashe auren. Hoto daga @bright_r
Asali: Twitter

Dukan ta ya yi a dakin otal din da suka kama za su yi bikin akan wani rikici wanda ba su bayyana ba ya shiga tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Hotunan tsoho mai shekaru 88 ya kammala digiri rana daya da jikarsa mai shekaru 23

An samu bayanai akan yadda mijin ya yi tatil da giya daga nan ya yanke shawarar datse batun auren inda ya fara dukan amaryar tashi.

Ba tare da bata lokaci ba, amaryar ta kwashe ya nata ya nata da ke cikin dakin ta tsere ana tsaka da shagulgulan auren.

Martanin jama'a

Labarin ya dauki hankalin mutane inda su ka dinga tsokaci karkashin wallafar.

@VieArr ta ce:

“bright_r, kada ka taba yarda da cutarwa a tarayya amma gaskiya ta dauki mummunan mataki kuma ta san ya sha giya ne, da bata dauki wannan matakin ba.. .Ta yuwu kuma ba karon farkonsa ne na dukanta ba.”

@hypemanoscar ta ce:

“Dukan su ba su da hankali ne halan? Bayan siya sutturu da biyan kudin dinki sai kawai ku datse igiyarsa cikin sa’o’i 10.”

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

@Mickyiv4 ta ce:

“Ta yuwu wannan ne karonsa na farko amma kuma ba na karshe ba, matakin ta ya yi daidai. Da zarar kin ga cutarwa ki kara gaba.”

@Grace tace:

“Giya bata mayar da kai azzalumi, kawai tana bayyana zaluncin ka ne. Tana bayyana asalin halayyarka. Ko wannan ne karon farko ta yi daidai da ta hakura da auren. Kada mutum ya yarda da cutarwa.”

Magidanci ya gwangwaje mijin tsohuwar matarsa da kyauta, bidiyon su ya taba zukata

A wani labari na daban, wasu maza biyu sun zama ababen kwatance bayan irin yadda su ka nuna kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu wacce ba a samu a wurin maza sai dai dai.

Daya yana auren wata mata ne wacce tsohuwar matar dayan ce, amma kyakkyawar alakar ta su sai da ta ba mutane da dama mamaki.

Cikin jin dadi ya siya wa mijin tsohuwar matarsa wani takalmi mai kyau da kuma kayatarwa.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

Asali: Legit.ng

Online view pixel